Written by Jamil Usman
- Babbar matsalar mata a zamanin nan ita ce bakar kazanta da rashin kula da jikinsu matukar anyi aure.
- Wannan mummunar dabi'ar kazantar na sa mace ta tsufa tare da ba miji hanyar neman matan banza a waje.
- Dabi'ar kazanta na sa miji ya dinga kyamar matar shi ta yadda baya iya cin abincin da ta girka ballantana a kai ga kwanciyar aure.
Sau da yawa auri saki ya fi ta'azzara tare da yawa a kasar hausawa. Hakazalika ganin karamar yarinya ta tsufa cikin shekara daya ko biyu bayan aure ya zama gama-gari. Yarinya budurwa tana yin aure, haihuwa daya zuwa biyu take yi ta zama wata uwar mata. A lokacin da take tashen budurcinta kuwa, zaka ganta yarinya sharaf mai aji, kwalliya, tsafta ga iya kame jikinta.
Ba wani abu ke tsufar da matan ba da ya wuce kazanta. Mata da yawa bayan sunyi aure su kan yada makaman kwalliya, tsafta, gayu da kame jikinsu. Suna kuwa haihuwa daya, biyu zuwa uku suke tsufa kamar sun haifa mazan nasu.
Sau da yawa sai ka ga mazan sun fara bibiyar 'yan mata masu tashe ko kuma karuwai a gari. Daga bisani idan ya ga dama sai ya kara aure ko kuma ya saki ta gidan saboda ba zai iya rike mata biyu ba.
Maza masu tarin yawa suna da kyankyami ta yadda basu iya cin abincin kazaman mata marasa gyara jikinsu.
Namiji mai imani da son matar shi ne yake iya zaunar da mace ya sanar da ita matsalarta don ta gyara. Wani kuwa sai dai ya kyaleta shi kuwa ya nema wa kan shi mafita.
Idan kazantar mace ta kai ta kawo, gashin kanta, fatarta da dukkan jikinta babu mai iya rabarta.
Mijinta baya iya zuwa kusa da ita ballantana a kai ga auratayya tsakaninsu. Amma abinda zai ba mutane mamaki shine yadda matan ke cin gayu tare da gyara jikinsu matukar zasu fita anguwa.
Wadannan matsalolin na sa mace ta tsufa cikin lokaci kankani kuma yana kashe aure.
Abin mamakin kuwa shine yadda suke komawa mata masu kula da jikinsu bayan sun koma gidan iyayensu. Daga nan wani ya dauka ya aura bai san matsalar kazanta ba ce ta hana ta zaman gidan mijin.
Gareku mata,a dage da gyara jiki da tsafta komai yawan yara. Tsakanin kazanta da tsafta mintoci kadan ne ko sa'o'in kadan. Sa'a uku kacal zasu isa mace ta gyara jikinta da dakinta tare da yaranta. Kuiya da lalaci kuwa basu barin wasu matan, kamar yadda jaridar Leadership Hausa ta ruwaito.
© Sirrinrikemiji
Post a Comment