Fitacciyar jaruma Kannywood, Fatima Isah Yola, wadda aka fi sa ni da Teemah Makamashi, ta ce sai da ta sha wahala ta gaske kafin ta samu daukaka a cikin masana'antar fina-finai ta Kannywood.
Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar ta da majiyar mu ta Northflix.
Jarumar Ta ce " Gaskiya daman ance sai an sha wuya a ke shan dadi, kuma mahakurci mawadaci. Gaskiya na sha wahala matuka, kuma na yi gwagwarmaya sosai a cikin masana'antar fina-finai, domin a baya na sha fita na sha wahala, wasu su biya ni, wasu kuma su hana ni kudin aikin da na yi musu, duk da haka dai na jure na ke yi saboda na san wata rana sai labari. To ka ga yanzu da na yi hakurin sai ya zame min alheri. Domin a yanzu duk wanda zan yi wa fim to cikin girma da mutunci ya ke zuwa ya same ni, kuma mu yi ciniki da shi, har ya fara ba ni wani kudi daga cikin kudin aikin tun kafin a fara aikin". Inji Teemah.
Ta Kuma ce" Wannan abun sai ya ke ba ni mamaki, domin a baya ka yi a hana ka kudin ka a kan lokaci, ko kuma a rinka ba ka kudin da guntu-guntu, wasu ma saboda rashin tsoron Allah sai ka yi aikin su hana ka kudin ka, to ka ga duk wannan abun a yanzu ya zama tarihi ". A cewar Jarumar.
Mun kuma tambaye ta cewar a yanzu kin zama babbar Jaruma ana ganin ki mai ajin da ko dai kin fi karfin yin fim ko kuma ba kowa za ki yi wa fim ba ya ki ke ganin wannan batun?
" To ina gani aji daban kuma sana'a daban kuma ka sani mutunci ne ya ke jawowa mutum haka, domin na mutunta kai na shi ya sa ka ke ganin a na shakka ta domin na san na gaba da ni, duk wanda ya ke gaba da ni zan ba shi matsayin sa. Idan kana sana'a zan ba ka matsayin ka na sana'a, to wannan ne ya sa a ke kallo na a matsayin wata mai ji da kai".
Ko wanne irin Nasarori Teemah Makamashi ta samu a harkar fim?
" To gaskiya babbar nasarar da na samu, ita ce arzikin jama'a, domin kuwa na samu arzikin ta sanadiyar  jama'a, ba dan su ba to da ba zan same shi ba, kuma na shiga wuraren da badan arzikin jama'a ba, shi ma ba zan iya shiga ba, domin haka zan iya cewa, ribar da na samu a cikin harkar fim ita ce arzikin jama'a, kuma ina alfahari da hakan". Inji Teemah.

Daga karshe ta yi kira ga 'yan fim da su hada kan su domin ceto masana'antar daga cikin halin da ta ke ciki a yanzu, domin dawo da martabar fim da kimarsa.


©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top