Wata matar aure mai suna Ruth Anthony a jiya Litinin ta bayyanawa wata kotu dake zama a garin Nyaya, Abuja cewa su gayawa mijinta mai suna Peter ya ba ta takarda saboda ba ta so ta yi kisan kai da sunan ceton ranta.

Matar ta bayyanawa kotu cewa mijinta yana da zafin rai. Inda a koda yaushe suka samu matsala yana yawan dukanta.

"Akwai lokacin da ya bi ni da gudu ni kuma na shiga kicin na dauki wuka, amma duk da haka ya shake min wuya, ni kuma na yanke shi a hannu", cewarta.

Matar ta kara da cewa don haka ne take kira ga kotu da ta sa mijin nata ya sake ta kafin ta yi kisan kai da sunan kare kanta.

A nasa bangaren, Mijin ya musanta zargin da matar tasa take yi masa, inda ya roki kotun da kada ta amshi bukatar matar tasa na neman ya sake ta da ta yi, inda ya ce yanzu ya canja halinsa.

A karshe dai Alkalin, Shittu Mohammed ya shawarci ma'autmratan da su daidaita tsakanin su idan sun koma gida. Sannan kuma ya daga sauraren karar har zuwa ranar 30 ga wannam wata na Janairu, 2020.

Post a Comment

 
Top