Daga Safwan Adam Burtuwa

Babbar murya zuwa gare ki kakkyawar mace, musamman, mai saka tufafin mai nuna tsiraicin jiki, saboda ki ja hankalin samari.

To barin baki wannan sirrin, mu (samari) mun san duk dalilin da ya sa kikeyin haka, mun san abinda ke tafe da ke, da abinda kike nema a wajen mu. Nan take za mu auna ki, mu gane halinki tas, sabida haka, kada ki yaudari kanki.

Duk mutum nagari, ba zai taba auren macen da take saka tufafi mai nuna tsiraicin jikin ta a bainar jama'a ba. Mijin ki da Allah ya hadaku tare ne kadai ya kamata ki saka wadannan kayan a gaban sa, amma kina bin titi-titi, layi-layi, lungu da sako duk kina tallata tsiraicin ki, wai kuma har kike fatan gamo da miji na gari?

Duk Diya mace Allah ya halicceta da sura mai kyau, saka kananun kaya, masu nuna tsiraici ba zasu taba Kara maki kyau ba, illa dai su rage maki daraja da kima, su jawo maki bala'i da tsana.

Kin san me samari ke so da ire-irenki ?

Za su nemeki da aure, amma ba auren ki za suyi ba, yaudara ce da neman daman yin lalata da ke, bayan sunyi, zasu gudu su baro ki, su nemi wata mai saka tufafi irin naki, itama suyi lalata da ita su barta a nan, aikin su kenan...

Ko iyayen su ba zasu taba yarda da yayan su, su auri Yar iska ba, su ma samarin masu irin wannan mummunar dabi'a basa yarda da auren irin ki ba.

Sirri zan baku. Amma zan fada da manyan haruffa: πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
Samari yan iska kadai ke son yan-mata masu adon tsiraici, Amma saurayi na gari ya tsani yar iska, karuwa, matar kowa da kowa.

Samari masu aikata haka Allah ya shiryesu, yan-matan kuma Allah ya ganar da ku. Allah ya tsaremu da iyalenmu, daga wannan fitinar karshan DUNIYA.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top