*MAGUNGUNA GUDA UKU ( 3 )*
•1 TSORON ALLAH:
Tsoron Allah yana daga cikin ibadu masu girma da ake yi da zuciya. Allah ya ce, “Wancan Shaixan ne yake tsoratar da ku masoyansa, kada ku ji tsoronsu, ku ji tsorona in kun kasance muminai” (Al-imran : 175)
A cikin wannan aya akwai abin da yake nuna wajabcin tsoron Allah shi kaxai, da qarfafa cewa hakan yana cikin lawazim na imani, gwargwadon imanin bawa gwargwadon tsoronsa ga Allah.
An karvo daga uwar Muminai Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, Na tambayi Annabi (S.A.W) akan wannan aya : “Waxanda suke bayar da abin da aka ba su zukatansu suna jin tsoro” Su ne waxanda suke shan giya, suke sata? Sai Manzon Allah ya ce, “A’a yake ‘yar Siddiq, su ne waxanda suke azumi suke sallah, suke sadaka, amma suna tsoron kada ko ba a karva daga gare su ba”. (Tirmizi ne ya rawaito shi)
Abubuwan Da Suke Kawo Tsoron Allah
1-Girmama Allah, saboda da saninsu ga sunayen Allah da siffofinsa.. “Suna tsoron Ubangijinsu a samansu” (Annahli : 50)
2-Tsoron kada makoma ta kasance abin da ba a so, na azaba mai raxaxi a cikin wuta, tir da wannan makoma.
3-Jin gazawa wajen sauqe wajiban da suke kansa, tare da riskar cewa Allah ya san komai kuma yan gani kuma yana da iko, da rashin ganin qanqantar zunubi fiye da ganin girman wanda aka savawa.
4-Tuntuni game da zancen Allah wanda yake cike da alqawarin azaba da tsoratarwa ga wanda ya savawa Allah, ya bar shari’arsa, da barin hasken da aka aiko shi da shi.
5-Tuntuni game da zancen Allah da Manzonsa, da duba tarihin Annabi (S.A.W)
6-Tunani akan girman Allah mai girma da buwaya, duk wanda ya yi tunani a kan haka, zai ga sifofin Allah mai girma da buwaya da girmansa, kuma duk wanda zuciyarsa ta hararo girman Allah zai san girman tsoratarwarsa, to ba makawa zai ji tsoron Allah. Allah ya ce, (Allah yana tsoratar daku kansa) (Al-Imran : 28)
Allah mai girma da buwaa ya ce, (Ba su girmama Allah ba yadda ya cancanci a girmama shi, qasa gabaxayanta damqarsa ce ranar alqiyama, sammai kuma suna naxe a damansa) (Azzumar : 67)
Tsoron Allah yana lazimta saninsa, sanin Allah yana lazimta tsoronsa, tsoronsa kuma yana lazimta yi masa xa’a
7-Tunanin mutuwa da tsananinta, kuma babu mai guje mata “Ka ce mutuwar da kuke gujewa za ta riske ku”. (Al-jumu’a : 8)
Wannan yana haifar da tsoron Allah, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Ku yawaita tuna mai katse jin daxi, babu wani wanda zai tunata yana cikin matsatsin rayuwa face sai ta yalwata masa, ko wanda yake cikin yalwa face sai ta quntata masa” (Xabarani ne ya rawaito shi)
8-Tuna abin da yake bayan mutuwa, na qabari da abubuwan ban tsoronsa. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Na kasance da na hanaku ziyarar maqabarta to ku ziyarceta yanzu, haqiqa tana sa gudun duniya, kuma tana tinatarwa ga lahira”. (Ibnu Majah ne ya rawaito shi)
An karvo daga Bara’u ya ce, “Mun kasance tare da Manzon Allah (S.A.W) a wata jana’iza, sai ya zauna a gefen qabarin, ya yi kuka har sai dai ya jiqa qasa, sannan ya ce, “Ya ‘yan uwana saboda irin wannan ku yi tanadi”. (Ibnu Majah ne ya rawaito shi)
Allah mai girma da buwaya ya ce, “Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku, kuma ku ji tsoron wata rana da uba ba ya isarwa da xansa da komai ba, ko wanda aka haifa ba zai iya isarwa wanda ya haife shi da komai ba. Haqiqa alqawarin Allah gaskiya ne, kada rayuwar duniya ta ruxe ku, kada mai ruxi ya ruxe ku game da Allah” (Luqman : 33)
•2 MANZON ALLAH (S.A.W) YACE IDAN ZAKU KWANTA KU RUFE DUK ABUBUWAN SHAN KU, DOMIN A CIKIN KWANAKIN SHEKARA WATA CUTA TANA SAUKA.
Duk abubuwan mu na amfani sai mu rufe su 🍶🧉 .
•3 HABBATUSSAUDA DA ZUMA:
manzon Allah ( s.a.w ) yace habbatusauda tana Magani duk wata cuta sai ( tsufa KO mutuwa ).
Za'a dafa habbatusauda kamar shayi ☕ sai a zuba Zuma cikin habbatusauda insha Allah tana Magani duk wani cuta idan Allah yaso.
© Sirrinrikemiji
Post a Comment