- Masu karatu barkanmu da wannan makon a cikin filinku na Hantsi Leka Gidan Kowa. 

 Yau tsaraba ce ga mata kan abubuwan da ya dace su sani game da mazajensu na aure.

Da farko kafin mu yi nisa, ya kamata mace ta yarda mijinta shi ne shugaba a kanta (wannan wajibi ne a zabi ba), ko da kuwa ta girme shi da shekaru, ko ta fi shi kudi, ko ilimi, ko matsayi, ko karfi kodai wani abu na rayuwa. Ki tuna fa shi ne ya je har gidan ku ya nuna sha’awar kasancewa tare da ke na tsawon wani lokaci da ba shi da karshe sai fa in mutuwa ta zo. Shi ne yake da hakkin kula da ke dangane da ci, sha, tufafi, matsugunni da kuma biya miki bukatar da babu wanda ya isa ya biya miki banda shi.


Akwai abubuwa da dama wadanda mata ya kamata su sani game da mazajensu, ga kadan daga cikin su kamar haka:


Yin kasa da sauti in kina magana da shi: Mace ta gari ita ce wacce ba ta daga muryarta idon tana magana da mijinta, ko da kuwa ran ta ya baci. Yin hakan zai iya fusata shi kuma ta yiwu ma har ya yi abin da bai kamata ba. Idon kika fahimci cewa ya hau sama wato ransa ya baci, sai ke kuma ki sauko kasa.

Ki ba shi hakuri in kin yi masa laifi: Dole ne mace in ta yi laifi ta bada hakuri. Wasu matan in sun yi laifin ma aka fada musu sai su fara musu, suna kokarin kare kansu. Mace ta gari ita ce wacce in ta yi laifi za ta yarda ta yi kuma ta bada hakuri.
Daukar shawararsa: Idan mijin ki ya baki shawara a kan wani abu ya kamata ki girmama ra’ayinsa in har bai ci karo da addinin ba. Wannan shi zai tabbatar masa da cewa kina girmama shi.


Wannan yana da matukar muhimmanci. Wasu matan kafarsu kamar tana musu kaikayi, miji yana fita za su dauki gyale sai gidan makwafta ko gidan kawaye. Gaskiya hakan ba hali ne na gari ba.

Ki sani dole ne in za ki fita, ki fita da izinin mijinki, kuma wajibi ki tsaya a iya inda kika ce za ki je. Wasu matan za su tambayi izinin zuwa gida daya ko biyu, amma za su iya shiga gidaje goma.


Idon kina fita aiki, ya kamata ki kiyaye ka ki daga abokan aikinki, ki rike amanar mijinki a wurin da baya nan. Wasu mazajen sun amince wa matansu amma su matan za su iya cin amanarsu. Ki sani fa wasu mazan za su rinka kula ki ko da kuwa sun san kin yi aure kuma sun san mijin naki, musamman ma in kina da kyau kuma ke fara ce, kin san mafi yawan maza suna son farar mace har ma za ki ji wasu suna cewa “fara ko ‘yar gidan sarkin mayu ce”. Dole ki lura da irin wadannan domin komai kamun kanki sun san yadda za su shawo kanki domin ki kula su.


Su ma matan da suke fita aiki, ku ji tsoron Allah in kun fita daga gida kar ku tsaya ko ina sai wajen aikinku, haka kuma in kun dawo kar ku tsaya a ko ina sai gidanku. Wasu matan suna amfani da aikinsu sai su shiga kasuwanni su yi ta yawo da sunan sayayya suka je. Gaskiya hakan ba shi da kyau. Ki tuna fa yaranki in sun dawo daga makaranta suna bukatar ganin ki, haka kuma mijinki ma in da wuri yake dawowa daga wajen aikinsa yana bukatar ganin ki tare da kulawa daga wajen ki.

Ya kamata mata su tuna cewa aure Ibadan Allah ce, yana da kyau su kyautata wajen zamantakewa da miji.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top