wai shin meyasa yan film basajin kunyar daukan hoton da bai dace ba?

wai shin meyasa yan film basajin kunyar daukan hoton da bai dace ba? musanman lokacin da suke kan daukar shirin fina finan su wato a location

idan jamaa basu manta ba sunsan yanda manyan malamai suke kalubalantar harkar film a munbarin su ko kuma a makarantun su wasu dayawa suna ganin wadannan malamai akan dede suke wadannan kiraye kiraye wasu kuma akasin hakan,

so da dama akwai bada kaloli dayawa dasuka faru a wannan masana anta a shekarun da suka gabata, idan jamaa basu manta ba sunsan yanda jaruman musammman mata suke jawowa wannan masana anta magan ganu,

kama daga kan jaruma rahama sadau da Amina amal da kuma sauran wadanda yanzu bai kamata a anbaci sunansu ba sakamakon aure da sukayi, maza kuwa abun nasu za a iya cewa bai taka rawa ya karya ba inbanda a kwanakin baya da sabuwar jarumar nan sadiya haruna tai tonan silili ga jaruminnan isa a isa,

ayanzu de za a iya cewa wannan harka ta film kullum dada ci baya take domin kuwa ayanzu zaa iya cewa kasuwar wadannan fina finai ta mutu murus wasu dayawa suna ganin wadannan dalilai sune suka dadda kawowa wannnan harka nakasu,

amma fa dayawa shuwa gabannin wannan masana anta da kuma wasu jarumai suna ganin wannan masaana anta tana nan a inda take bata mutu ba,

mun tattauna da wani darakta dake cikin wannan masana anta wanda ya nemi a sakaye sunansa ya bayyana mana cewa wannan matsaloli sun faru ne sakamakon zalinci da rashin rukon amana da suke tsakanin mu
mun tambayeshi wanna irin zalunci kenan kake nufi?

yayi mana bayani kan cewa tun lokacin da ake kasuwar kaset zaka ga mutun yazo da kudinsa ai masa film amma sai kaga wasu daga cikin masu shirya fina finai sun cinye wannan kudi ko kuma za a kashe miliyan daya a film amma sai kaga sun ce miliyan daya da rabi zaa kashe,

sannan bayan an gama wannnan kwamacala aka dawo kai fina finai gidan tv se kaga anse film din mutun dubu dari shida amma sai suce masa dubu dari hudu aka siya to wadannan sune ma za a iya cewa suna da adalci a cikinsu abunda yasa nace haka kuwa wasu idan ka basu film dinka sukai gidan tv se kaga idan an biya kudin sai ka nemesu ka rasa,

dama de ance muddin zaku dunga zaluntar na kasa daku to babu inda zakuje to gashi tun baaje ko ina ba har kar gidan tibun ta mutu,

Post a Comment

 
Top