Daga Datti Assalafiy
Fitaccen Malamin addinin Musulunci Ash-sheikh Assistant Professor Dr Mansur Isah Yelwa Bauchi (H), Babban Limamin Masallacin juma'a na jami'ar ATBU Bauchi, Kuma babban Lecturer a jami'ar Ado Bayero University Kano, ina tsamman shine HOD na Faculty of Islamic Law (idan ban manta ba), kwararren masani ne a bangaren Shari'a Mahaddacin Qur'ani da Hadisai kwararre a fagen Tafsirin Al-Qur'ani Maigirma.
Yau juma'a 31-1-2020 Malam yayi khudubar juma'a a Babban Masallacin juma'a na ATBU akan matsayin hukuncin kisa da kotu ta yanke wa Maryam Sanda wacce ta hallaka mijinta Bilyaminu.
Malam ya ga cewa akwai fa'idah mai amfanarwa ga jama'ar Musulmi sai ya yanke shawaran yin khduba na musamman sai kowa ya amfana, tunda matsalace da ta shafi kasa gaba daya, kuma Musulmai suna bukatar sanin menene matsayin Musulunci akan wannan.
A cikin khudubar Malam yayi gamsasshen bayani a fannoni kamar haka:
1- Me ya jawo Maryam Sanda ta aikata wannan aika-aika?
2- Yanzu bayan hukunci ya tabbata akan Maryam Sanda, shin yaya wannan hukunci yake a mahangar addinin Musulunci?
3- Yaya matsayin wannan matar Maryam Sanda a yanzu da aka yanke mata hukunci?
4- Yaya matsayin addinin Musulunci akan irin wannan hukunci?
5- Yaya matsayin addinin Musulunci akan irin nau'in zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya da za'a mata?
6- Hukuncin da aka yankewa Maryam Sanda da dokar da ba na Musulunci ba idan an zartar zai zama mata kaffara a gurin Allah?
7- Bayani akan girma da munin kisan-kai a Musulunci.
8- Bayani akan nau'ukan kisan kai da ake aikatawa a mu'amala na yau da kullun.
Allahu Akbar! Wallahi addinin Musulunci akwai dadi da zunzurutun adalci, don Allah duk wanda ya samu khudubar da zan daura yayi kokarin yadawa zuwa ga inda ya dace saboda akwai dunbin fa'ida wanda ya kamata duk wani Musulmi ya fahimta.
Allah Ya sakawa Malam sakamako da gidan Aljannah Amin.
Zaku samu wannan audio da kun latsa wannan link Domin saukar da audion a wayoyinku.
©HausaLoaded
Post a Comment