Wani malamin addinin Kirista kuma dan kasuwa mai suna Apostle Chris Omashola ya ce Maryam Sanda ba za ta mutu ta hanyar rataya ba

- A ranar Talatar da ta gabata ne wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga Maryam Sanda

- Malamin ya ce bai san dangin ta ba amma su ci gaba da addu'a don Ubangiji ya nuna mishi ba za ta mutu ta hanyar rataya ba

Wani malamin addinin Kirista kuma dan kasuwa mai suna Apostle Chris Omashola ya bayyana abinda ya hango game da Maryam Sanda, matar da ta kashe mijinta.legit na ruwaito.

A ranar Litinin ne wata babbar kotun tarayya da ke zama a Maitama Abuja  ta yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta sameta da laifin kisan kai.


Babbar magana: Allah ya nuna mini cewa ba za a rataye Maryam Sanda ba - Babban Fasto
A yayin yanke hukunci a kan shari'ar, Mai shari'a Yusuf Halilu, ya kama ta da laifin abinda ake zargin ta da shi.

'Yan sanda sun zargi Sanda da sukar mijinta da fasasshiyar kwalba wajen karfe 3:50 na safiyar ranar 18 ga watan Nuwamba, 2017.


Amma Apostle Omashola wanda cikin kwanakin nan ya bayyana 'wahayin' shi a kan mawaki Naira Marley, ya je shafin shi na tuwita a ranar Talata tare da sanarwa a kan Maryam Sanda ba za ta mutu ta hanyar rataya ba.

Kamar yadda ya ce, Ubangiji ya nuna mishi cewa Maryam Sanda ba za ta mutu ta hanyar rataya ba, kamar yadda jaridar The Nation Online ta ruwaito

A shafin malamin, ya rubuta: "Ban san 'yan uwan Maryam Sanda ba. Jiya ne kawai na ci karo da maganar. Ta ci gaba da addu'a don na hango cewa za ta rayu. Ubangiji ba zai bar ta ta mutu ta hanyar rataya ba. Ban san ta yadda abin zai faru ba amma na hango hakan a wajen bauta. Ku taya ta da addu'a".

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top