Abinda kowa ya kamata ya fahimta shine kafin a zartarwa Maryam hukunci tana karkashin beli ne, wato ba'a gidan yari take tsare ba, an bayar da belinta, wallahi wasu kwanaki da suka gabata da idona na ga Maryam Sanda da Mahaifiyarta da 'dan da ta haifa, da kanin mijinta marigayi Bilyaminu a wani guri a cikin garin Abuja, har nayi zaton cewa an kammala Shari'ar gaba daya.

Da aka zo zaman kotu a yau, bayan da kotu a matakin Federal High Court ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya, sai alkali ya bayar da umarni a tafi da ita gidan yari kafin ranar rataya ya cika, sai dai dokar gwamnatin Nigeria ya bata damar daukaka kara zuwa Court of  Appeal har zuwa Supreme Court.

Hukuncin High Court ba shine karshen al'amari ba a halin da Maryam Sanda take ciki, akwai matakin sake zama a kotuna guda biyu da na fadi a sama, hatta Alkalin da ya zartar mata da hukuncin kisa a yau sai da ya bata damar daukaka kara idan ta ga dama.

A tsarin kundin dokokin gwamnatin Nigeria sashi na 241 cikin baka na (1) ya bada dama ga wanda aka yanke masa hukunci idan bai gamsu ba ya daukaka kara har zuwa Kotun da ga ke sai Allah Ya isa, wato Supreme Court.

Sannan a dayan bangare tsarin mulkin Demokaradiyyah da ake yi yau duniya har da Nigeria, tsari ne da yake kiyayya da batun zartar da hukuncin kisa ga wanda ya aikata laifin kisa kamar Maryam, lallai ko shakka babu zata samu kariya anan duniya, da wahala a kashe ta a iya abinda na fahimta da kuma hange.

Bayan haka Mahaifiyar Maryam mai kudi ce kuma 'yar siyasa, babu shakka ko da arzikin da ta mallaka a duniya zai kare zatayi hakan don ta kubutar da 'yarta daga fuskantar hukuncin kisa anan duniya, sannan kungiyoyin kare hakkin bil'adama masu gaba da irin wannan hukunci na kisa zasu iya kawo mata agaji su kubutar da ita.

Amma ko a yanzu "an tauna 'kasa domin aya taji tsoro!", wannan babban izna ne ga masu tunanin daukar mummunan mataki na kisa a lokacin da suka fusata, biyewa zuciya na kai ga mutum zuwa ga nadama marar amfani.

Idan Maryam Sanda ta aikata laifin kisan Mijinta da niyya a cikin zuciyarta kashe shi tayi niyyar yi da gaske, to tabbas bata da wani zabi face sai ta dandana azabar hukuncin kisa a nan duniya ko kuma a Lahira ranar da Allah Zaiyi hukunci da kanSa, amma idan bisa kuskure ne ta kashe mijinta, ba niyyarta ta salwantar da rayuwarsa ba, to har a gurin Allah Maryam tana da zabi na tuba da biyan diyyah.

Sai nake ganin kuskure ne mu tabbatar da cewa Maryam da gaske tayi niyya a zuciyarta ta kashe mijinta ne duk da ance wuka ta daba masa, sannan kuskure ne mu yarda cewa ba da gangan ta kashe shi ba, Allah ne Kadai ya san abinda ta kudurce a ranta, Ya kuma san yadda akayi Mijinta Bilyaminu ya rasa rayuwarshi a sanadiyyarta.

Muna rokon Allah Ya sa mu fi karfin zuciyarmu a cikin kowani irin hali Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top