Wani binciken masana a ƙasar Amurka ya nuna cewar akwai sinadarai da ke ƙara ƙarfin ƙwaƙwalwa waɗanda ke cikin ƙwai.


Binciken masana a kan bin diddigin kan sinadaran da ke ƙunshe cikin ƙwai ya nuna cewa matuƙar mutum na cin kwai aƙalla guda uku kullum na iya kaucewa da kamuwa da gigin tsufa.

Binciken wanda sashen bin diddigin ya tabbatar da cewa hatta mata masu ciki na buƙatar suna cin ƙwai wanda zai rage musu yawan laulayi da kuma ƙarawa jaririn da ke cikinsu lafiya.

Haka kuma suka ce ƙwai na ɗauke da sinadarin Cholesteral wanda yake yaƙar cutar maiƙon jinin jikin ɗan adam.

Jami ar Oxford da ke ƙasar UK ta shirya samar da hanyoyin wayar da kai don ganin an buƙasa yadda za a samar da kwai a kullum.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top