Fasihin mawakin siyasa da ke Kano, Dauda Kahutu Rarara ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa an kona shagonsa na daukar wakoki da ke Zoo Road a Kano.
Mawakin ya kuma musanta jita-jitar da ke yawo cewa an kai masa hari don a kashe shi.

Mawakin ya musanta jita-jitar ne a lokacin da ya tattauna ta wayar tarho da wakilin Aminiya a ranar Alhamis da ta gabata.
Ya ce, “Ban san komai a kan batun jita-jitar ba.”

An yada jita-jitar cewa a ranar Talatar makon jiya wadansu ’yan bindiga sun kai wa mawakin hari a shagonsa na daukar waka da ke titin Zoo Road a Kano, inda aka ce Rarara ya tsira amma kuma mahararan sun kona masa shagonsa.
Ya ce, “Wannan zance karya ne, ban san komai a kai ba, Bashir yau ka zo Najeriya ko Kano? Mutane za su yada jita-jitar a kaina saboda wata maunfarsu. Sun taba cewa na yi hadari har an yanke kafafuna da hannuna, sun ce an kona gidana saboda na yi wakar azanci ga Kwankwaso da kuma Shekarau, ina so mutane su sani jita-jita ce babu gaskiya a ciki.”
Mawakin ya ce a yanzu yana cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.
“Ina cikin halin koshin lafiya da kwanciyar hankali, a yanzu ma ina shagona na daukar waka don yi wa Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje sabuwar waka ta lashe zabe.” Inji Rarara.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top