Tsohuwar fitacciyar jarumar nan ta kamfanin shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Fati Muhammad, ta bayyana auren jarumi Sani Musa Mai Iska a matsayin babbar nadamar ta a rayuwa.

Jarumar ta bayyana hakan ne a wata hira da tayi da jaridar Blue Print inda ta bayyana cewa ta amince da cewa kowa na da jarabawar da Allah ya ke yi masa sannan kuma tace ita ta bangaren aure Allah ya jarabe ta.

Jarumar ta kara nanata maganarta as tayi a baya inda tace ba fa zata kara auren dan fim ba koma wanene kuwa.

Daga karshe kuma jarumar ta bayyana jarumi Ali Nuhu a matsayin wanda take darajawa fiye da kowa a masana’antar fim.

Post a Comment

 
Top