Fittacen malamin addinin Musulunci a Najeriya Alaramma Ahmed Suleiman ya bayyana irin ukubar da suka shiga a hannun masu satar mutane don kudin fansa.
An yi garkuwa da malamin ne a ranar 14 ga watan Maris kan hanyar karamar hukumar Kankara a jihar Katsina da ke arewacin kasar.
Amma a ranar Alhamis 27 ga watan Maris rundunar sojojin Najeriya ta ceto shi da sauran mutane biyar da aka yi garkuwa da su.
Rundunar sojojin Najeriya sun ceto fitaccen malamin kungiyar Izalan nan a Najeriya Alaramma Ahmed Suleiman da sauran mutane biyar da aka yi garkuwa da su.
Da yake jawabi a fadar sarkin Katsina jim kadan bayan ceto shi, Malamin ya ce al'amarin mummuna abun tunawa ne. "Sai dai Alhamdulillahi tun da Allah ya kwato mu," in ji shi.
Ya kara da cewa: "Kullum su kan ce mana ai tun da yanzu aka ce hukuma ta shiga to Malam ba za ku koma gida ba, ko an kawo kudin nan sai mun kashe ku.
"Kullum ba abin da muke ji a kunnuwanmu sai kalmar za a kashe mu, sannan a yi ta harba bindiga a gabanmu. Gaskiyar magana kwanaki ne masu wahala sosai,' in ji Malam Ahmad.
Malamin ya kuma ce: "Sai dai hakan jarabawa ce kuma darasi ne. Ubangiji kan jarraba bawa don daga darajarsa ko yafe masa wasu zunubansa.
"Ina gode wa Allah da rundunar sojin Najeriya da kuma malamanmu na kungiyar Izala.
"Haka muke taruwa ni da yaran mu yi ta kuka," in ji Malam Ahmad.
Ya kuma ce sai da ya sauke Al-Kur'ani mai girma har sau shida a kwanakin da suka shafe hannun mutanen.
Sojojin sun bayyana cewa tun bayan garkuwa da malamin, shugaban hafsan sojin kasar Laftanar Janar Tukur Buratai ya ba runduna ta 17 ta sojojin kasar umarnin ceto malamin.
Sojojin sun ce sun yi amfani da dabaru iri-iri da suka hada da tattara bayanan sirri da kuma aiki kafada da kafada da sauran jam'ian tsaro wajen ceto malamin.
Sun bayyana cewa a yanzu haka malamin da sauran malaman da aka yi garkuwa da su na cikin koshin lafiya bayan likitocin sojojin sun duba lafiyarsu.
Har ya zuwa yanzu, babu wani karin bayani kan ko an kama wadanda suka yi garkuwa da malaman ko ba a kama su ba.
BBChausa.
Post a Comment