Hajara Isah Jalingo, fitacciyar jarumar fina-finan Hausa ce, inda ta yi manyan fina-finan Ingilishi na Kannywood kamar su ‘This is the Way’ da ‘Light and Darkness’ da kuma ‘There’s A Way’. A wata tattaunawar kafa sadarwa da wakilin Aminiya da kuma shafin Twitter na Kannywoodscene suka yi da ita, ta bayyana yadda tafiyarta ta kasance tun lokacin da ta shigo harkar fim da shawarar da iyayenta suke ba ta a kullum. Jarumar wadda ta lashe Gwarzuwar Jaruma Mai Tasowa a Gasar City People Entertainment Awards a shekarar 2017 ta bayyana dalilin da ya sa take so jaruma Hadiza Gabon ta zama makwabciyarta. Ga yadda hirar ta kasance:
Yaya za ki kwatanta tafiyarki a masana’antar Kannywood?



Tafiya ce mai cike da hawa da gangara, na samu gogewa da kuma sanin makamar aiki a Kannywood, a zahirin gaskiya rayuwar Kannywood wata sabuwar rayuwa ce mai zaman kanta.
Wace shawara iyayenki suka ba ki lokacin da za ki fara harkar fim?
ADVERTISEMENT
Mamata takan yawaita fada min cewa, kin san tarbiyyar da muka ba ki, to ba sai na ce komai ba. Kai ma ka san wannan nasiha ce da ta kunshi komai, ba sai an yi ta maganganu masu yawa ba, kai ma ka san ana nufin komai za ka yi to ka ji tsoron Allah.
Tun wane lokaci kika fara sha’awar ki zama jaruma?
Tun ina da shekara goma sha uku na fara son fim, saboda akwai wani gidan nuna fim a Jihar Taraba da suka ce za su fara fim a Jalingo, sai na fada wa iyayena ina son in fara a nan tunda sun ki amincewa in je Kano, amma a wancan lokaci sai suka nuna rashin yardarsu, inda daga baya dai na samu suka amince in fara fim.
Mu koma batun fim din Ingilishi na ‘There is a Way’, a mutane sun ga kin yi kokari sosai, kin yi magana da Ingilishi cikin kwarewa har wadansu suke ganin kin haura babban mataki na karatu, shin hasashensu ya zama gaskiya?
Ni kaina na burge kaina, amma a zahirin gaskiya yanzu nake Difloma a Kaduna.
Wadanne abubuwa kike yi a lokacin da ba kya wurin daukar fim?
Nakan zauna in yi hira tare da abokaina ko in mayar da hankali wajen karatuna.
Wadanne jarumai ne suke sanya ki dariya?
Jaruma Jamila Nagudu da kuma Sadik Sani Sadik, idan kana tare da su dole ka yi dariya, suna da barkwanci da kuma haba-haba da mutane.
Wane irin abinci kika fi so?

Na fi son tuwo da miyar kuka ko shinkafa da mai da yaji.
Yaya kike mu’amala da masoyanki walau a kafar sadarwa ko idan kin hadu da su?
A gaskiya yadda suka zo mini haka nake mu’amala da su, idan sun zo da lumana in mu’amalance su ta hanyar lumana, idan sun zo da tsiya-tsiya sai in nuna musu ni ma fa ba kanwar lasa ba ce.
Wadansu suna ganin cewa akwai soyayya tsakaninki da jarumi Nuhu Abdullahi, ko me za ki ce a kan haka?
Ni ma haka nake ji, amma ban san da hakan ba.
Idan na fahimce ki babu ke nan?
Eh, babu.
Wane tufafi ko mota ko turare ko ’ya’yan itatuwa kika fi so?
Gaskiya a wannan bangare ba ni da wani zabi, duk wani abu da na gani mai kyau nakan so shi.
Wace jaruma kike so ki yi makwabtaka da ita?
Hadiza Gabon, saboda idan kana tare da ita ba za ka yi bakin ciki ba, ta iya sa mutane nishadi, mutum ba zai yi nadamar kasancewa kusa da ita ba.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top