![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjdM6rcZ8048tARZ-7fL4ILwj8HqXX_WW_pKdsoY-9Zp3xrXGzaK4-67qi5PIjpR0QHmEDSZyhTrU_OGJavG5HVnw7sJziczlqmpWx5A8UUWv8Th5MOWeygP_CyYVAnxYb8Hmu-Gsrwlq1a/s1600/ic-648.jpg)
Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta yi wani jawabi a shafinta na sada zumunta inda tace, daya daga cikin kalubalen da mutum ke fuskanta shine tarin makiya, ta kara da cewa saidai makiyine kawai zai yi maka gyara a lokacin da ka aikata ba daidai ba. Ummi tace amma matsalar shine idan aka tashi yin gyara sai a rika wa mutun ta yanda bazai dauka ba maimakon a yi cikin Nasiha.
Wasu mabiyan Ummin sun jawo hankalinta akan kayan data saka a wannan hoton inda sukace be dace ba ta daina.
Saidai ummi tace kayan nata basu sabawa shari'a ba in banda gashin kanta da ta bari a bude kuma tana samun babban mayafi ya rufeshi tsaf zata iyayin sallah a haka:
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEiewg9OoZlp6Hh1hTMetBxvC2HQK0KnRHyFstwIZsIh0bs600WypGSeXdnNKoHh3HkDpF79E6dQZk0vdsroFgoFJvWnnbrMxEftnYmPw6WOY2FQy_S-bnxjlzU7wPHq9kW9uu2xuTGwElAA/s1600/ic-2029.jpg)
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEiKb4dkSjovK73PuiRGWgIpSckkwQcvSnoU0sATcYKB817YX-dBgGplOME8F3o6Pr4R0nhiJ9-jPaQc5_mv9h3wGFBiz2fYdPcg3KVPqWhm59Y-x8bd-oDFyZdhDdld4XzrXZf_XZFJPJjN/s1600/ic-1302.jpg)
Post a Comment