KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA
GA MASOYA Idan kana tare da budurwa masoyiyar ka, ya kasance kanayi mata kalamai masu dadi na jan hankali, wadanda zasu dinga faranta mata rai.
KAMAR HAKA
Na dade ina kallon taurarin samaniya yayinda naga wacce tafi kowacce haske, saina naga bakowa bace nike ganiba sai ke masoyiyata So gamon jinine, haqiqa sonki ya zamo jinin jikina Kinfita daban a cikin mata.
duk lokacin da na kallleki, sai naga kamar babu kyakykyawar wace sai ke Ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu wata a zuciyata sai ke kadai Yarda da amincewarki gareni, sune zasu tabbatar da soyayyarki ta gaskiya a gareni.
Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, dan haka kowane hali nike bazan ta6a mantawa dake ba masoyiyata Nakan raba dare ina mai roqon Allah don neman biyan buqata,
Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a sama, kuma tayi saiwa a qasa, haka sonki ya mamaye dukkan jikina.
KALAMAN SOYAYYA
Ina ma a ce na kasance da ke a duk bugun numfashina, kaunarki ce take kara tasiri a ruhina, babban burina na ga bayyanar fitar murmushinki a kan wannan kyakykyawar fuskarki, ya kuma zamana ni ne sanadin hakan.
Bana son Allah ya kawo lokacin da za ki fushi da ni sosai kaina ba zai dauka ba, hakika Allah ya wadata ki da abin da mata da yawa suke nema sun rasa ke kanki kin san a cikin jinsinku, mata irinku kadan ne da a ce na iya rubuta labari da a kan fuskarki zan rubuta littafi mai suna kyauta daga Allah, kuma na san zan samu bayanan rubutu kamar guda uku 1,2 da Sararin samaniya na cike da taurari, teku na cike da ruwa, doran kasa na cike da ciyayi, amma ni zuciyata cike take da soyayyarki ba ta gushewa kamar yadda taurari ba sa gushewa a sararin samaniya, ba ta kafe wa kamar yadda teku ba ta kafe wa, haka zalika ba ta bushe wa kamar yadda ciyayi ba kamar sukan bushe, soyayyarki dauwamammiya ce a farfajiyar madinan zuciyata da akwai wanda zai tsaga jikina da ya ga jininki yana gudana, a kan kaunarki na manta kaina, kikan hau ingarman doki domin ki taho mafarkina, wannan sunan da kika boye a tafin hannunki idan dare ya yi, ki duba sararin samaniya kin ga mai wannan sunan yana haska duniya masoyiyata, hakika na kasance mai bayyana a mafarkinki kin kasance a fatar lebena. Duk wani taku da na yi a doran duniya sai inji takun na iso ni zuwa gare ki. So marurun zuciya ya yi min saka tun asali so ya shige zuciyata yana min suka.
Ganinki burina, idanuwana ko bacci na farka ki amshi soyayyata abadan kada na koka ba ni barinki cikin kunci yaki zo na yi miki tarba. Daga motsin numfashina kika ziyarci rayuwata a matsayin abokiyar rayuwa a duk zantukana sai na ambace ki. Damuwarki kullum tana cikin tinanina ke ce jin dadina kuma ke ce bacin raina ke kadai ce a zuciyata kalamaina, zabina jin dadina, bacin raina, saboda da ke kawai nake rayuwata, kaunarki ce ke kula da ni take kuma kau da duk wata damuwa daga raina koda a ce babu ni ka san tuwata zan zamana a tare da ke har abada. Kamar yanda baki bai isa ya furta ba haka jiki bai isa ya nuna ba, sannan zuciya ta yi kadan ta kwatanta ruhinki ne kadai ya san yadda nake jinki a sakamakon ziyartar da yake yi wa ruhina a kowane dare ina sonki ba zan daina ba har abada saboda ban isa na daina ba.
Soyayyata da ke ba ta mutuwa kuma ba ta tsoran mutuwa koda za a yi mana kwace, ko da za mu mutu ko za mu lalace to soyayyar mu za ta kasance a raye na bayar da zuciyata na karbi ta ki na kamu da sonki. Ki tallafi rayuwata da ta tsunduma a kan tsananin soyayyarki, ki tausayawa zuciyar da ta shagala a kan tsananin soyayyarki ka da rintsi ko zugar mahassada ya sa ki guje ni ko kuma ki rage son da kike min, sonki yana dankare a zuciyata kamar yadda kwakwalwa ke dankare a kan dan’adam da a ce zan samu ikon fito miki da shi da na yi domin ki kara gazgata tsananin kaunar da nake miki.
KALAMAN SOYAYYA MASU SANYA MASOYA MURMUSHI
TA ‘DAYA. Ina son dukkan taurarin da suke bisan sama, amma ba za’a hada son da na ke yi musu da kuma na wadda ta ke a cikin idanuwan ki ba, ina son ki.
TA BIYU. Lokaci yana nan zuwa da zaki mallakawa wani zuciyar ki, ina mai yin kira a gare ki da ki tabbatar da cewa kin mallakawa wanda ba zai raunata zuciyar ki ta hanyar yaudara ko cin amana ba, saboda ita zuciya d’ayace babu wadda zaki dauko ki sauya a lokacin da bakin ciki da damuwa suka mamaye zuciyar ta ki.
TA UKU. Yanzu haka ina cikin farin ciki, shin kin kuwa san mene ne dalili? Hmm saboda na kasance mai sa’a, kin kuwa san tayaya? Saboda Allah ya na so na, kin kuwa san me ya sanya na ce haka? Saboda ya ba ni wata babbar kyauta, kin kuwa san mene ne? Ba komai ba ne ba face KE masoyiyata, ina son ki.
TA HU’DU. A koda yaushe lokaci tashi yake yi tamkar tsuntsu, amma ita soyayyar mu kullum ginuwa ta ke tare da kara samun wajen zama a cikin zuciyoyin mu karda ki manta da ni ki kasance mai yin tinani na kamar yadda nima na kasance a ko da yaushe.
TA BIYAR. Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne kema na san kin san da haka cewa ina son ki, a duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa ko da nan da can ba, wannan shi ne abun da zai faru da ni a duk lokacin da na rasa ki.
TA SHIDA. SO tamkar wata sarkar zinari ce da ta d’aure zuciyoyin mu a waje guda, a dukkan lokacin da kika tsinka waccan sarka tofa ki tabbatar da cewa tamkar kin kore farin ciki ne daga cikin zuciya ta.
TA BAKWAI. Salim ina son ka, me ya sanya ka ke yin kokwanto a bisa kalmar so da na furta a gare ka? Tabbas kaine mutum na farko da haduwa da shi ya kore min bakin ciki, ya wanzar da farin ciki a zuciya ta ya yalwata murmushi a saman fuska ta hakane dalilin da ya sanya na ke kiran ka da SADAUKI. Salim, ka yi nasara ka yi nasarar jan ra’ayin soyayya ta a kan ka kaine na mallakawa linzamin zuciyata, kaine mutum na farko da na taba furtawa kalmar SO kuma a yanzuma zan kara mai-maitawa a gare ka ina son ka.
Ka amince mu yi tsaftatacciyar soyayya. Sai yanzu na gano cewa a duniya babu abun da ya kai samun masoyi dad’i, a duk lokacin da na rasaka ban san halin da zan shigaba, daga karshe ina mai sanar da kai cewa buri na yanzu bai wuce na ganin ranar da zaka zamo ango ni kuma na zamo mata a gare ka ba, ina alfahari da kai a duk inda na kasance, ka huta lafiya daga mai son ganin farin cikin ka a koda yaushe.
KALAMAN SO MASU FARANTA ZUCIYA BURINA MU KASANCE CIKIN INUWA ‘DAYA MASOYINA.
A cikin kowace safiya na kan tashi cikin farin-ciki saboda ina sanya ran a ko da wane lokaci zan iya ganin ka amma zuwan dare kan yi sanadiyar zubar hawaye daga idaniyata saboda lokaci ne da yake nisanta tinanina ga tsammanin sake ganin ka a koda wane lokaci kafin wayewar gari. Fatana ka fahimci cewa ina son ka ina kuma shiga damuwa a lokacin da na nesanta da kai. Ina ‘kaunar ka masoyina.
FATANA BAI WUCE
Ina son ki zamo mallakina a cikin mafarkina da kuma a zahiri, ki zamanto cikin hirata da sauran dukka zantukan bakina faruwar hakan zai inganta farin cikin zuciyata. Fatana a kullum ki gamsu da cewa, Ina Son Ki.
MUNA NAN TARE CIKIN DARE KO RANA MASOYINA.
Shin masoyina izuwa yanzu ko ka fara jin gajiya a jikinka kuwa? Saboda ka kasance kana motsi a cikin zuciyata a tsawon dare ka kuma kasance mai zagaya dukkan jikina ta kafar da jinin jikina ne kawai yake gudana a cikin kowace safiya da yini. Ina son ka.
KARDA KI NESANCE NI INA TARE DA KE.
Ko da ya kasance kin nesanta da ni, ni kuma zan kasance a tare da ke har abada, bakina kan gaza furta kowace irin kalma domin bayyana miki adadin yadda nake son ki a dukkan lokacin da muke tare amma cikin dare ko safiya zuciyata na bayyana min cewa, ke ce farin cikina, fitila mai kore duhun zuciyata, Zara kike tauraruwa cikin taurari. Ina son ki. ki huta lafiya.
INA SON BAYYANA MIKI CEWA
So tamkar hasken rana yake da yake haske fuskar da take d’auke a jikin gangar jiki ma’abociyar zuciyar da take ‘kunshe da So. Kasantuwar so a cikin zuciya kan motsa ruhi ya kuma busar da idanuwa daga barin yin bacci a mafi yawancin dare, So kan samar da wasu rassa a cikin zuciya bayan bayyanar sa, wato bakin-ciki da kuma farin-ciki. Zan ci gaba da son ki a cikin kowane irin yanayi. Ina Son Ki.
MU KASANCE TARE HAR ABADA.
Masoyiyata ina neman alfarmar da ki mallaka min zuciyar ki, na dad’e da mallaka miki tawa lokuta masu yawa da suka shud’e abokai ma shaida ne, bayan ya kasance kin mallaka min ita ni kuma zan had’a su na d’aure su waje guda da sarkar soyayya mai ‘karfi na jefa makullin a cikin tekun maliya. Ki amince ina son ki wannan shi ne burina. Ki huta lafiya.
SAMUN KI A RAYUWATA BABBAR NASARA CE.
Matata Uwar ‘ya’yana mai share hawayena tabbas samun ki a matsayin matata babbar nasara ce a rayuwata ga dangina da kuma duniya baki d’aya, ina cike da zumud’in son dawowa domin cin girkin ki mai dad’i. ki kula min da kan ki, sai na dawo. Ina son ki matata.
KO KIN SAN YAYA NAKE JI IDAN BANA TARE DA KE MATATA?
Nesantar ki babban aiki ne da yake jigata zuciyata, dama ace zaki iya fuskantar halin matsi da takura da nake shiga da kuma shaukin son kasancewa a tare da ke da nake ji cikin zuciyata a dukkan lokacin da na nesanta da gida. Ina fatan zaki ci gaba da kula min da kan ki har zuwa lokacin da zan dawo gida. Allah ya tsare min ke matata, ina son ki.
KALAMAN SOYAYYA NA MAZA DA NA MATA
{NA MAZA}
1} Fatan gushewar yunwa da sanyayar ruhi da tabbatuwar lada ga wadda tinaninta ke É—ebe min kewa a lokacin da nake galabaice ko a lokacin da nake tsaka da hutawa.
2} Kasancewar ki a tare da ni, ya sa ni jin kaina a matsayin wani mutum mai daraja ta musamman. Ina son ki, so irin wanda kalmomi ba zasu iya bayyanawa ba.
3} Na kasance cikin murnar zagayowar watarana, wato ranar da kika nuna amincewarki ga soyayyata. Ba na jin zan iya rayuwa ba tare da ke ba, saboda ke ce rayuwata, kuma ke ce mahaÉ—in numfashin da nake shaka.
4} Na kan yi mamaki a baya, a duk lokacin da na ga wani ya shiga matsananciyar damuwa a kan so, amma bayan haÉ—uwata da ke, na fahimci abun da ake kira da so. A halin yanzu, ni ma a shirye nake da na yi yaki da duk wanda ya yi kokarin raba ni da ke. Barka Da Shan-ruwa.
5} Matukar zan cigaba da kasancewa a tare da ke, ba na jin hatsarin da nake ji ana cewa so yana da shi zan gamu da shi watarana. Ke ta daban ce kuma ta musamman a cikin rayuwata. Ina Son Ki.
6} Kamar yadda zai yi wuya mutum ya manta da wani É“angare na jikinsa, haka ni ma zai yi wuya na manta da ke a rayuwata. Kin shiga zuciyata kin zauna, kin bi jijiyoyin jikina kin narke a cikin jinina. Ina Son Ki. Barka Da Shan-ruwa.
7} Burina a yanzu, bai wuce ganin na mallaki tauraruwar da haskenta ke haske sararin samaniya ba, a kowane dare. Wadda nake fatan ta haskake rayuwata da haske mara disashewa. Ke ce dai wannan É—in nan, wadda ke bayyana a cikin baccina, ko a lokacin da nake farke, da rana ko a cikin dare. Ina Son Ki.
8} Fatana a ko da yaushe, na gan ki cikin walwala da nishaÉ—i. Burina na ga fuskarki cike da fara’a da annushuwa. Fatan Kin Sha-ruwa Lafiya.
9} Ki kalli sararin samaniya, za ki gan ni tsaye a kusa da ke, domin kuwa, ni ma na yi hakan kuma na gan ki a kusa da ni, haskenmu na haska duniya. Ina Fatan Kin Sha-ruwa Lafiya? Na yi Kewar Ki.
10} Me zai hana ni kasancewa tare da wadda ta mallaka min zuciyarta? Wadda nake da tabbaci kan yadda take gudun ganin na shiga damuwa? Wadda ke tattalin farin-cikina? Wadda sautin muryarta ke cire min kasala da sanya ni yin bacci mai cike da mafarkai masu daÉ—i? Ba kowa ba ce wannan face ke! Ina Son Ki. Barka Da Shan-ruwa.
11} A dukkan lokacin da muka yi nesa da juna, na kan ji da ma a ce akwai manyan tsaunika a kusa da ni, da na hau ko zan samu na hango murmushin fuskar nan naki mai taushi. Na Yi Kewar Ki.
12} Wasu na gulmar, wai watarana za a wayi gari na ji son ki ya ragu a cikin zuciyata, idanuwana su daina ganin kyawunki, ni kuwa na ce, ba na fatan zuwan wannan rana ina mai numfashi a doron ‘kasa. Ni a kullum, ina jin sonki ne na karuwa a cikin zuciyata, a dukkan lokacin da muke tare ko muka nesanta da juna. Ina Son Ki.
13} Na ji tsoron mafarkin irin mummunan halin da zan shiga a duk lokacin da na rasa ki. Zamowa ta cikakken mutum zai kammala ne a ranar da kika zama mata a gare ni. Ina Son Ki.
14} HaÉ—uwarmu ta kasance ne bisa ‘kaddara, zamowar mu masoya ya faru ne bisa zaÉ“inmu, amma ba wa son ki gurbi a cikin zuciyata, ya zama dole ne a gare ni, saboda kin zamo wani É“angare na rayuwata, haka kuma tinaninki ya zama masarrafin sarrafa akalar rayuwa da tinanina. Ina son ki, so irin wanda gangar jiki take yi wa ruhi.
15} Yunkurin sanin adadin yadda nake jin son ki a cikin zuciyata, da dalilan da suka sa nake kaunar ki, a gare ni, daidai yake da a ce na bayyana irin É—anÉ—anon da ruwa yake da shi. Tabbas abu ne mai matukar wahala.
16} Kina da dabaru na sanya ni yin murmushi ko da a ce ina cikin fushi ne. Kin zamo wata ta-daban a gare ni. Ina son ki, so mara iyaka.
17} Kina da kyau masoyiyata, fiye da yanda kike gani a madubi. Kyawu ne irin wanda babu wani furuci ko zanen wani mai zane da zai iya fasalta shi. Ina Son Ki.
18} Ina fatan mafarkin da na yi jiya, ya maimaita kansa a cikin baccina na yau, mafarkin da nake fatan ya zamo gaskiya, mafarki ne da a cikinsa na gan mu a tare a matsayin miji da mata.
19} Ganin shigowar sakonki cikin wayata, na canja yanayin da nake ciki daga damuwa izuwa farin-ciki, ba komai bane ya jawo hakan face tsantsar son ki da ke killace a cikin zuciyata. Ni ne dai naki a kullum…..
20} Kafin na haÉ—u da ke, kalamaina na da saukin samuwa ga kowace mace, amma a halin yanzu babu wata mace daga cikin jerin ‘yammatan birni ko na karkara da zata samu irin kulawar da na shirya ba ki a tsawan rayuwar zamantakewarmu, daga yanzu har izuwa karshen rayuwata. Ke ce wadda na zaÉ“a, nake fatan mu kasance tare har abada. Ina Son Ki.
{NA MATA}
1} Zuwa ga zaɓin zuciyata, ina fatan ka sha ruwa lafiya? Ina fatan izuwa yanzu nutsuwa ta game jikinka, ishiruwa ta gushe daga makoshinka? Ina kuma fatan lada ya tabbata a gare ka.
2} A dukkan lokacin da na ga daren Lailatilkadari, zan kasance mai rokon Ubangiji Ya mallaka min kai a matsayin mijina uban ‘ya’yana, ina fatan kai ma zaka kasance mai tsawaita tsayuwa cikin kowane dare domin ganin cikar burinmu? Ina Son Ka.
3} A lokuta da wurare daban-daban ina ganin ka kana yi min gizo, ina ganin ka a lokacin da idanuwana ke a rufe ko a buÉ—e. Ba na iya yin komai ba tare da tinaninka ba.
4} Jin muryarka na sakwan guda, na jefa ni cikin kogin tinaninka, na tsawan lokacin da idanuwana ke kasancewa a buÉ—e.
5} Irin kulawar da kake nuna min a kullum na saka ni tinanin irin yadda rayuwarmu za ta kasance a nan gaba. Zan zamo tamkar sarauniya a gidanka, kai kuma zaka zamo sarkin da babu wani mai irin masarautarsa a duniya ta kowace fuska. Ina Son Ka.
6} Zuciyata ba za ta taɓa canja matsayin da kake da shi ba a cikinta. Murmushina gare ka ba zai taɓa yankewa ba. Son ka a cikin zuciyata ya yi kafuwar da ba zai taɓa goguwa ba a cikinta na har abada.
7} Da a ce zan iya zama komai, da na zama ruwan hawaye a gare ka, a haife ni a cikin idanuwanka, na rayu a saman kumatunka, na mace a saman laɓɓanka. Ina son ka so mara misaltuwa. Barka Da Shan-ruwa.
8} A dukkan lokacin da kake bukatar wani ya taya ka hira, karda ka manta kana da ni, ka nemo ni domin É—ebe maka kewa a cikin kowane irin yanayi da lokaci.
9} A lokacin da na tino irin rayuwar da na yi a baya, na kan hango irin asarar da na yi, na kasancewa ta ni kaÉ—ai ba tare da kai ba , yanzu na same ka, ina ji na a matsayin wata wadda ta fi kowace mace sa’a a rayuwa. Ina fatan na kasance a tare da kai na har abada.
10} Ba zan taɓa mantawa da ranar cikar burina ba, ranar da wanda nake so ya nuna min soyayyarsa a fili, ba kowa bane face kai hasken idaniyata. Ina son ka.
SOYAYYA TSAKAIN MAAURATA
ℳa'aurata suna daukar duhun Kai ko in ce girman Kai a kan nuna wa junansu soyayya bayan AURE. Wanda yana Daga cikin Babban gibin da auren yake samu. Misali. Ya kamata na miji ya dinga daurewa ko kakane yana nunawa matar sa soyayya. Yana gaya Mata maganganun soyayya ❤ irin su.
♡ INA SONKI ♡ INA KAUNARKI ♡ KE CE MACEN DA NAFI SO A DUNIYA ➜ ko Kazan nan yayi miki kyau da dai sauran maganganun na nuna soyayya da kulawa. Wanda haka zai sa taji itama ba ta da masoyi daya fi shi. Kuma wannna kalmomin ba zasu taba bacewa ba a cikin kwakwalwarta. Kuma zasu ta dinga yawan nishadi da jin ita Mai sa'a ce a rayuwar aurenta.
➽ AMMA DAN ALLAH KANA NUNA MATA IRIN HAKA A RAYUWAR AURE KU ? ◦ DAN UWA KA GYARA KADA KA BARI TA DINGA JI A BAKI WASU HAKAN ZAI BATA DAMAR TSANA A RAYUWAR AURE KU.
☛ HAKA idan mace ce take gayawa mijinta Yar uwa soyayya bata tsufa a wanna rayuwa koda kina da shekara 80 kice masa.
yallabai Ina son ka. ❊ dear I love you. ❊ Kai ne mijin da kafi kowanne birge Ni. ❊ ko ta ce ai Ni duk wani Abu da kake so Ina son shi. ❊ ko in zai fita kice Allah ya dawo min da Kai lafiya. ❊ ko in yayi kwalliya kice kayi kyau fa darling. Da sauran maganganun nuna soyayya da kambama shi kina nuna yafi kowa.
Post a Comment