Saduwar aure babban ginshiki ne ko kuma a ce jigo ne a cikin zamantakewar aure wanda idan ana samun tangarda a kai walau ta bangaren mata ko mijinta, yana da matukar wahala zaman aure ya yi dadi. Wani abin haushi ne, sau tari za ka ga ana samun matsala ta wurin mata a kan saduwar aure.
Wata matsalarta ba ta cika so ba, wata matsalarta rashin sanin yadda za ta yi wa maigida domin jindadinsu baki daya, wata matsalarta ma sai miji ya yi da gaske kafin ya shawo kanta ta amince ya kwanta da ita, wata kuwa ma ta mayar da saduwar aure kamar wani abu da yake amfanar da miji shi kadai ban da ita.
To masu irin wannan dabi’ar, su sani cewa ba ga miji kadai saduwar aure ke amfani ba, har su kansu akwai amfanin da suke samu idan suka yi saduwa da mazajensu. Filin Taskira ya yi muku nazarin irin muhimmancin da saduwar aure ke da shi ga mata:
(1) Saduwan aure yana maganin tarin gajiya (stress), idan kina da wata tattaunawa (interbiew) kamar gobe ko za ki yi magana a wani taron mutane, bincike ya nuna wadanda ke saduwan aure akalla sau biyu a sati sun fi yin wani abin kirki.
(2) Saduwan aure yana sanyawa a samu barci maidadi mai kuma inganci kuma a samu lafiya,saboda zuciya ta samu natsuwa da sauran abubuwa .
(3) Saduwan aure yana maganin ciwon kai, in kina fama da ciwon kai to saduwa tana maganinsa.
(4) Saduwan aure yana maganin mura wadda sanyi ya kama ki, sannan yana ba da kariya ga jiki daga kamuwa da sanyi wanda ka iya haifar da mura.
(5) Saduwan aure yana hana tsufa da wuri, bincike na kiwon lafiya ya nuna duk matar da ke saduwa, a duk shekara 12 tana komawa ‘yar shekara 7.
(6) Saduwan aure yana sanyawa mace ta rika samun saukin yin period (jinin al’ada), da yawa ‘yan mata suna fama da ciwo yayin period amma da sun yi aure sai su nemi ciwon babu.
(7) Saduwan aure yana canza ma mace yanayin tsarin jikinta inda kasusuwanta zasu kara girma da wasu sassan jikinta.
(8) Saduwan aure yana kara ma zuciya lafiya, sanin ku ne ciwon zuciya shi ne ciwon da ya fi kashe mata a duniya, cin abinci mai inganta lafiya da rage kitse suna taimakawa sannan saduwan aure yana taimakawa wajen magance zuciya daga kamuwa da ciwo.
(9) Kwanciyar aure yana kara ma mace lafiya a kwakwalwarta sannan ya cire mata bakin ciki da damuwa ya sanya ta nishadi.
(10) Saduwan aure yana taimakawa wajen inganta lafiyar ‘bladder’ ga mace.
(11) Saduwan aure yana sa mace ta ringa jan hankalin Mijinta saboda saduwa a kai a kai yana sa kyan fata da bakin gashin kai har da tsayi ma. ‘Yan’uwa mata sai himmatu wurin gyara abubuwan da za su kyautata wannan ibada ta aure. Allah ya taimake mu baki daya amin, mu a hadu a mako mai zuwa, insha Allah.
© Sirrinrikemiji
Post a Comment