Tun shekara ta 2003 da Buhari yafara siyasa jihar kano itace jihar da duk shekarar zabe sai mun bashi kuri'a saboda miliyan daya, babu jihar da take zaben Buhari kamar kano har jihar katsina.
Bayan kaci zabe sai da kayi shekara biyu bakazo kano ba, kuma lokacin da kazo haka kafita baka yiwa mutanen kano jaje ba da ta'aziyya ta mace-mace da gobarar da akayi a kasuwar sabon gari.
Amma haka muka sake zabenka a Karo na biyu muka baka kuri'ar da babu wata jiha data baka duk Nigeria kuma mutanen wasu jihohin suka dinga zaginmu suna gayamana magana suna cewa bamu iya siyasa ba saboda babu abinda kayi mana na aiki Amma muka zake zabarka.
A jihar Lagos Bola Tinubu cewa yayi baya son gwamna mai ci, Amma a haka kana gani Bola Tinubu yakawo Wanda yakeso yayi Takara a jam'iyyar kuma yasamu nasara saboda jihar Lagos ce.
Kowa yasan irin aikin da CP Walili yayi kafin zabe, yakawo tsaro a kano kuma ranar da akayi zaben farko yayi aikinsa nisa ka'ida batare da goyon bayan gwamnati ba.
Amman saboda rashin imani irin na gwamnatin APC kuma turo kadiri, zindiki, Mara imani Wanda bai San darajar Dan Adam ba yazo yanawa gwamnati dama yayi amfani da yan daban suka dinga sukan mutanen gari suna saransu saboda kawai ka farantawa yarabawa rai.
Yanzu wannan ne abinda zaka sakawa mutanen jihar kano dashi kenan? Duk irin halaccin da mukayi maka wannan shine sakamakon zaben da mukayi maka?
Mutanen kano sun zabi abinda sukeso kai kuma mace bashi kakeso ba shine kuma turomana mutane marasa imani suka karbi tsaron a hannun CP Wakili bawan Allah, mutane miliyan biyu sukayi zabe lafiya a zabe na farko Amma a jiya kuri'a dubu Dari da wani abuce zatayi zabe akayi rashin imani Wanda bamu taba gani ba a tarihin siyasar jihar kano.
Kuma duk saboda bukatar yarabawa a shekara ta 2023 kayi kana haka saboda kai bazaka sake zuwa kano campaign ba.
Wannan bala’i da aka sanyamu a ciki ba zamu taba yafewa ba wallahi. Allah yana gani kuma ba zai taba kyalewa ba. An ce ana yakar rashawa amma an fi son dan rashawa akanmu saboda ana tsoron jam’iyya za ta fadi. Duk duniya ta yi Allah wadai da wannan ta’addanci amma Buhari ko a jikinsa. Sai nan gaba zai zo ya ce ai baya gari aka yi tun da dama haka ya shirya
©HausaLoaded
Post a Comment