Sanata Bala Mohammed, dan takarar gwamnan jihar Bauchi a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ya lashe zaben kujerar gwamna bayan an kai ruwa rana tsakanin sa da gwamna mai ci, Mohammed Abubakar, na jam’iyyar APC.
Bayan tattara sakamako da hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) ta yi a yammacin ranar Litinin, an sanar da Bala Mohammed a matsayin wanda ya samu nasarar lashe kujerar gwamnan jihar Bauchi.
Dakta Musa Dahiru, sabon baturen INEC, ya ce PDP ta samu kuri’u 39,225 yayin da jam’iyyar APC ta samu kuri’u 30,055 daga sakamakon zaben raba gardama da aka yi a jihar Bauchi.
Sakamakon zaben ya hada da na karamar hukumar Tafawa Balewa da aka dade ana ta gumurzu a kan sa.
An tantance adadin ma su kada kuri’a 74,181 daga cikin mutane 139,240 da ke da katin zabe. An samu jimillar sahihan kuri’u 73,041 yayin da kuri’u 738 su ka lalace.
Da ya ke sanar da sakamakon zaben na karshe, Dakta Dahiru ya bayyana cewar sanata Bala Muhammad ya samu jimillar kuri’u 515,113 da suka bashi nasara a kan Muhammad Abubakar, wanda ya samu kuri’u 500,622.
An cigaba da tattara sakamakon zaben ne bayan wata kotun gwamnatin tarayya dake Abuja ta ki amincewa da bukatar dakatar da INEC daga cigaba da tattara wa da sanar da sakamakon zaben da aka maimaita a jihar Bauchi. Alkalin kotun, Jastis Inyang Ekwo, ya zartar da hukuncin ne a ranar Litinin (yau).
Da yake yanke hukunci a kan zaben, Jastis Inyang, ya bayyana cewar kotu ba ta da hurumin shiga maganar.
©HausaLoaded
Post a Comment