A wani rubutu da na taba yi mai taken: The Chronicle of Tension, Kano State vs Kano Emirate, na bayyana asalin yadda zamantakewa ke kasancewa tsakanin gwamnati da Masarautar Kano, tun daga zamanin sarkin Kano Abbas 1904 har zuwa lokacin sarkin Kano Ado.

Asali tun bayan nadin Sarkin Kano Abbas aka fara samun matsala tsakanin gwamnatin turawan mulki, da masarautar Kano. Musamman akan ofishin wazirin Kano. A yayin da turawa suka yi karfa-karfa suka cire babban dan sarkin Kano Abbas; Abdullahi Bayero suka mai da shi chiroma suka nada Wani Bawa mai suna Alabar Sarki a matsayin wazirin Kano. Wannan Shi ya janyo wata katuwar baraka da ta kusan tafiya da sarkin Kano Abbas, har sai da Gwabna Luggard ya sanya baki. Wanda daga Karshe dai aka kwabe Alabar Sarki aka nada Muhammad Gidado dan malam Mustapha a matsayin wazirin Kano.

Abin mamaki shine; rikicin nadin Waziri shine dai ya zama rikici na karshe a zamanin jikansa: Sarkin Kano Ado.

A zamanin sarkin Kano Sanusi, wannan rikici ya kara kunno kai, tsakanin gwamnati da Masarautar Kano, sai dai ba kamar a zamanin sarkin Kano Abbas ba, a wannan lokaci gwamnati tayi nasarar cire sarkin. Sai dai duk da wannan nasara da Gwamnati tayi, har yau Kanawa na kallon abinda ya faru a matsayin zalunci ga masarautar Kano. Hakan kuma ya kara jawowa gwamnati tsangwama da zubewar kima a jihar Kano, a wannan lokaci.

Bayan rasuwar sarkin Kano Inuwa, nadin Sarkin Ado ya zo da batutuwa da dama na rikice rikice, musamman daga matsalar ‘yan movement for Kano State, da kuma ‘yan Tijjaniya da sauransu. Juyin mulkin 1966 da kuma zuwan mulkin soja ya kara tayar da rikici tsakanin gwamnatin Kano karkashin Audu Bako da Sarkin Kano Ado, cikin yardar Allah, abubuwa suka zo cikin sauki daga karshe, inda aka sulhunta bayan an fahimci daga inda matsalar take.

Amma fa ba wai rikicin gwamnati da masarauta ya kare ba kenan, domin zuwan gwamnatin siyasa a zamanin jamhuriya ta biyu, daga 1979 zuwa 1983, ya zo da wata sabuwar mummunan alaka tsakanin gwamnatin PRP (santsi) da masarautar Kano. Tsakanin Gwamna Rimi da Sarkin Kano Ado. Wannan rikicin yafi kowanne muni, domin an rasa rayuka an kuma samu asarar dukiyoyi, cikin wadanda wannan fitina ta tafi da rayukansu harda shahararren masanin nan kuma mai ba Gwamna Rimi shawara akan harkokin siyasa Dr Bala Muhammad, an kuma kona majalisar dokoki ta jihar Kano, wadda a yanzu ta zama asibitin yara na Hasiya Bayero.

A yanzu haka a wannan zamani, ta fito fili akan babu kyakkyawar alaka tsakanin Gwamna Ganduje da Maimartaba sarkin Kano Muhammad Sanusi II. Duk wani yunkuri da Mai martaba sarki yayi na shawo kan matsalar, abin yaci tura.

Wasu na ganin wannan matsalar ta samo asali ne daga wasu makusantan gwamnan da suke ganin zasu amfana in rikicin yayi tsamari, musamman wasu makusantan gwamnan dake da alaka da gidan sarautar. Wasu kuma suna ganin, jajircewar da sarki yayi akan kawo gyara a yadda ake tafiyar da gwamnatin. Hakan ne dai ya taba faruwa a zamanin Gwamna Rimi da wasu daga cikin gidan sarautar suka kara rura wutar gaba tsakaninsa da sarki Ado, saboda suna ganin zasu amfana da rikicin.

Koma dai da me, batu na gaskiya, tarihi yana maimaita kansa, kusan a duk wani yunkuri da akayi na tab’a sarki a Kano, yana zuwa da abubuwa marasa dadi.

Abinda wasu ba su sani ba shi ne har yau wasu na kallon abinda ya samu su Sardauna da cewar dalilin tab’a sarautar Sarkin Kano Sanusi na daya ne.

Ni a fahimtata, da kuma dogon nazarin da nayi, tun daga kan Festin (Wanda shine DO na Kano a zamanin sarkin Kano Abbas), zuwa jamhuriya ta farko, Wanda a lokacin aka yi rikicin cire Sarkin Kano Sanusi na daya, har zuwa kan gwamnatin Rimi da tayi yunkurin cire sarkin Kano Ado, babu wacce acikinsu ta k’are lafiya.

Festin dai sai da yayi haukan da ya kona gidansa da kansa, shekaru bayan rikicin cire Sarkin Kano Sanusi Gwamnatin ta kife, duk da irin shahara da goyon bayan da Rimi yake da shi, amma bai koma gwamnati ba, saboda wannan yunkuri da yayi na tab’a masarautar Kano. Wannan gargadi ne, in kunne yaji, jiki ya tsira.

A fahimtata, Gwamna Ganduje ya hau kan karagar mulki a karo na biyu, ta wata barauniyar hanya, Wanda ta ragewa karfin gwamnati kima a idanun mutane. A matsayinsa na shugaba kuma dattijo, abinda ya kamata shine kokarin sulhu da kuma daukar matakan kwantar da hankalin jamaarsa, bawani lokaci da Kano ke bukatar zaman lafiya kamar yanzu, rigima da masarautar Kano ba abu ne da zai haifawa gwamnatinsa da mai ido ba. Ya zama wajibi, ya tashi tsaye ya nemi sulhu da masarautar da kuma abokan adawa, sannan ya zo da sabbin tsare-tsare da zasu yaki talauci da lalacewar tarbiya da ke addabar talakawan Kano, musamman a bangaren noma, da ilimi da samar da ayyukan yi, da sauransu.

Fatanmu shine Allah ya zaunar da Kano lafiya, domin duk wani yunkuri na taba masarauta a wannan lokaci abu ne da zai jawo fitintinu da tashe tashen hankula a jihar Kano. Hakan kuma a Karshe zai jawo zubda jini, halakar rayuka da salwantar dukiyoyin jamaa. Wanda ba wata gwamnati da zata so haka ya faru.

Muna fatan gwamnati zata duba ta fahimci illar dake tattare da wannan mataki, ta hana masu yada labarai marasa tushe acikin mutane, ta kuma yi kokarin sasanta mutane domin a samu a rage wannan zaman dar-dar da ke cikin zukatan talakawa a Kano.

Allah ya ja zamanin sarki
Allah ya zaunar da jihar kano lafiya. Allah ya taimaki Nijeriya.

Amin!!!

Fatihu Mustafa
Rariya.

Post a Comment

 
Top