Fittacen malamin addinin Musulunci a Najeriya Alaramma Ahmed Suleiman ya bayyana irin ukubar da suka shiga a hannun masu satar mutane don kudin fansa.
An yi garkuwa da malamin ne a ranar 14 ga watan Maris kan hanyar karamar hukumar Kankara a jihar Katsina da ke arewacin kasar.
Amma a ranar Alhamis 27 ga watan Maris rundunar sojojin Najeriya ta ceto shi da sauran mutane biyar da aka yi garkuwa da su.
Rundunar sojojin Najeriya sun ceto fitaccen malamin kungiyar Izalan nan a Najeriya Alaramma Ahmed Suleiman da sauran mutane biyar da aka yi garkuwa da su.
Da yake jawabi a fadar sarkin Katsina jim kadan bayan ceto shi, Malamin ya ce al'amarin mummuna abun tunawa ne. "Sai dai Alhamdulillahi tun da Allah ya kwato mu," in ji shi.

An yi garkuwa da mutane da dama a Zamfara
Nigeria: Evans ya amsa lafinsa na 'satar mutane' a kotu

Ya kara da cewa: "Kullum su kan ce mana ai tun da yanzu aka ce hukuma ta shiga to Malam ba za ku koma gida ba, ko an kawo kudin nan sai mun kashe ku.
"Kullum ba abin da muke ji a kunnuwanmu sai kalmar za a kashe mu, sannan a yi ta harba bindiga a gabanmu. Gaskiyar magana kwanaki ne masu wahala sosai,' in ji Malam Ahmad.
Malamin ya kuma ce: "Sai dai hakan jarabawa ce kuma darasi ne. Ubangiji kan jarraba bawa don daga darajarsa ko yafe masa wasu zunubansa.
"Ina gode wa Allah da rundunar sojin Najeriya da kuma malamanmu na kungiyar Izala.
"Haka muke taruwa ni da yaran mu yi ta kuka," in ji Malam Ahmad.
Ya kuma ce sai da ya sauke Al-Kur'ani mai girma har sau shida a kwanakin da suka shafe hannun mutanen.

Sojojin sun bayyana cewa tun bayan garkuwa da malamin, shugaban hafsan sojin kasar Laftanar Janar Tukur Buratai ya ba runduna ta 17 ta sojojin kasar umarnin ceto malamin.
Sojojin sun ce sun yi amfani da dabaru iri-iri da suka hada da tattara bayanan sirri da kuma aiki kafada da kafada da sauran jam'ian tsaro wajen ceto malamin.
Sun bayyana cewa a yanzu haka malamin da sauran malaman da aka yi garkuwa da su na cikin koshin lafiya bayan likitocin sojojin sun duba lafiyarsu.
Har ya zuwa yanzu, babu wani karin bayani kan ko an kama wadanda suka yi garkuwa da malaman ko ba a kama su ba.

Me kungiyar Izala ta ce?
Kungiyar Izala ta kasa a Najeriya ta bayyana farin cikinta game da kubutar da Sheikh Ahmad Sulaiman da rundunar sojin kasar ta yi.
Sai dai bayanan da BBC ta samu ya nuna cewa ba a kama kowa daga cikin masu garkuwa da mutanen ba.
Wata majiya ta sojin ta shaida wa BBC cewa an gayyaci sojojin ne domin taimakwa wajen gano malamin, kuma a shirye suke su ci gaba da taimakwa domin ganin an shawo kan matsalar wadda ke addabar sassa daban-daban na kasar.
Kimanin makonni biyu da suka wuce ne aka kama Sheikh Ahmad Sulaiman yana kan hanyarsa ta komawa Kano, a wani yanki na jihar Katsina, kuma masu satar mutanen a baya suka nemi a biya su daruruwan miliyoyi kafin sakinsa.
Sheikh Abdullahi Bala Lau shugaban kungiyar ta Izala ta kasa ya bayyana wa Ahmad Abba Abdullahi yadda suka ji da sakin malam Ahmed:
Matsalar Garkuwa da mutane ta dade tana ci wa 'yan kasar tuwo a kwarya a fadin kasar.

©Bbchausa.com

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top