Abin nufi shi ne ka da mace ta kusanci da namiji har sai ta yi aure. 

Zamani ya zo zinace –zinace sun yawaita a sanadiyyar wayoyi da yanar gizo-gizo.

 A zamanin nan ba a jin kunyar zina, haka ba kasafai aka damu da in an kai amarya a bincika shin cikakkiyar budurwa ce ko ta sayar a waje sabanin da da ake zuwa a shinfida farin kyalle a daren farko, da safe a zo a duba har ma a yi yekuwa duk gari su ji cewa wance ‘yar wane ta ci bantai ma’ana an same ta cikakkiyar budurwa.

Amma duk da haka ‘yan matan da su ka sami wannan matsala su kan shiga dimuwa a duk lokacin da bikinsu ya karato cewar su na so su sha maganin da zasu hade su dawo sababbi fil a leda kamar ba’a taba yi ba. 

Ashe kin san barna ki ka tafka ba daidai ba ne. Iyayenki da ‘yan uwanki mata ba su sani ba, ba ki isa ki tare su ki ce su like ki ba saboda kin san laifi ne, dan haka sai ki dinga bin kawayenki da su ka taba yin aure da amaren unguwarku alhali ba za su rufa miki a siri ba su ne masu zuwa su yayata ki. 

Shin akwai kuwa abinda budurwa za ta sha ta dawo sabuwa fil?

Babu shi sai dai a kwatanta a rurrufa amma fa in har ango ya san abinda ya ke yi zai gane.

Su waye ma su aikatawa ‘yan mata wannan ta’asa?

Samari ne matasa da kuma dattijai wadanda sun haife su wasu sun yi jika da su. Wannan ta’a sa ba sunan ta fyade ba, saboda da yardar yarinya aka yi har ma an biya ta ko kuma an saya mata abin duniya kamar sabuwar waya mai tsada, kayan kwalliya, kwamfuta da sauransu. Wata kuma a dalilin ba ta so ta ci tuwo miyar kuka ya sa ta bayar da mutuncinta, sai ya saya mata shawarma, gassashen kifi, tsire, pizza da dai sauransu.

 Wata kuwa babu ko sisi dalilin tsabar kauna da take yiwa saurayin ya yaudare ta da dadadan kalamai na soyayya wadanda ya binciko a yanar gizo-gizo kalaman indiyawa da nasara, bayan ya sami kanta sai ya guje ta daga ta kira waya sai ta ji shiru.

Aikata haka ya na da illa ko nasara ce?

Illa ce babba saboda duk wanda ki ka yarda ya sanki a waje ba zai yarda ya aure ki ba, kuma shine mai bada mummunar shaida a kanki don ka da ma wani ya aure ki, shine mai tara abokai ya suffanta mu su yadda halittarki ta ke, daga kin fito a bi ki da kallo ana yi miki kallon fanko. 

Ko da kuwa ya aure ki babu in da auren zai je saboda ba zai taba yarda da ke ba sai zargi kullum. Idan kuwa daban ne ya aure ki ba tare da ya sani ba, ya na ganin haka zai tsane ki kuma ba za ki sake daraja a idanuwansa ba haka ba zai yi wa iyayenki kallon mutunci ba.

Idan samarin ba su saka miki ciwon kanjamau ba ciki zai iya shiga ba za ki yarda ki haife ba sai ya kai ki a zubar, daga nan kin kara rugurguza rayuwarki a matsayinki na budurwa kin zubar da ciki dan haka surarr jikinki ta kwararrabe duk kwaskwarimar ki sai an gane.

Ina mafita?

Iyaye sai sun saka ido sosai akan ‘yayansu mata, tun su na kanana har zuwa lokacin girmansu. Babban abin da uwa za ta shi ne ta yi ta tsorata yarinyarta a kan ka da ta yarda wani da namiji ya kirata , ki tsorata ta da ciwon kanjamau ake dauka idan aka sadu , ki tsorata ta da mutuwa ake idan namiji ya san ta kafin ta yi aure, ki ce mata wari za ta dinga yi kowa sai ya gane ko da a boye ta yi.

Ta na girma ki na bin ta da shawarwari, ki fara cusa mata tsoron Allah a zuciya, da misalai masu tsoratarwa. Idan ta fara al’ada abu na farko da za ki fara jan kunnenta shi ne ka da ta kuskura ta kusanci namiji tana zuwa ciki zai shiga. Haka ki gargade ta da ka da ta bi gurbatattun kawaye da samari. Duk kawa ko saurayin da ba ki yarda da tarbiyyarsa ba ki raba su. Ki san lokacin zuwa da tashinta daga makaranta ka da ta yi miki karyar lokaci daga can ta zarce yawo ki yi zaton tana makaranta. Ka da ki bar ta da waya mai tsada a cikin wayar nan ne makarantar shaidanu ta ke. A guji yiwa yara baki, a bi su da addua ta alkhairi.

Shawara ga ‘yan mata:

Duk yadda iyayenki su ka jajirce kun fi kowa sanin in da za ku bullo mu su ku yi wayo ku je ku yi aika-aika, to ki sani ba iyayenki kadai ki ka cuta ba kanki ki ka cuta duniya da lahira. Dan haka a kame kai har sai an yi aure.

 


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top