Jam'iyyar PDP ta yi zargin cewa hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta kama membanta wanda shine mataimakin shugaban kwamitin yakin neman zaben ta na shugaban kasa, watau Barista Tanimu Turaki.

Me magana da yawun PDP dinne, Kola Ologbondiyan ya fitar da sanarwa a dare Litinin cewa EFCC sun kama Tanimu Turaki inda ya bukaci da su gaggauta sakinshi ba tare da gindaya wasu sharuda ba.

Ya kara da cewa, tunda PDP tace bata yadda da sakamakon zaben shugaban kasa ba kuma ta sha alwashin zuwa kotu da hujjoji masu karfi, sai hankalin APC ya tashi suke amfani da hukumomi dan ganin sun tsorata PDP akan zuwa kotun.

Yace EFCC ta kama Turakine bayan da ta gayyaceshi bisa tsayawa Babalele Abdullahi dan bayar dashi beli amma sai shima ta rikeshi bisa wasu hujjoji marasa tushe.

Yace duk wannan abu dake faruwa bazai taba hana PDP zuwa kotu ba dan kwatowa Atiku zabenshi da Buhari ya kwace dan cika burin 'yan Najeriya

Post a Comment

 
Top