Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ba zai damu ba ko da ya fadi zaben gwamna da ake kan gudanarwa yau Asabar.
Gwamnan ya na fuskantar dan takarar jam’iyyar PDP, Isa Ashiru ne, wanda ake ganin su biyu ne za su fafata a zaben.
Da ya ke amsa tambayoyi, ya ce shi ba ya cikin wata fargabar cin ko faduwar zaben gwamna da ake kan yi a yau a garin Kaduna.
Ya ce tunda dai Shugaba Muhammadu Buhari ya ci zaben shugaban kasa, to a na sa bangaren idan ta yi ruwa rijiya, idan ma zaben gwamna bai yi ruwa ba, sai ya maida ramin ya zama masai.
“Ni ba ni wani zaman dardar din jiran sakamakon zabe. Mafi munin abu dai ai a ce na fadi zabe.
To idan na fadi ba ni da kaico, tunda dai Shugaba Muhammadu Buhari ya rigaya ya ci zaben shugaban kasa, to bukata ta biya.”
“Ma’aikata na da makusanta da hadimai na ne ke kwana cikin fargaba. Amma ni ban damu ba.”
Haka ya shaida wa manema labarai bayan ya jefa kuri’ar sa da karfe 8:30 na safe, a rumfar zaben sa da ke Unguwar Sarki, Kaduna.
Premiumtimeshausa.
Post a Comment