Matashinnan dan jihar Kano, Mubarak Bala wanda ya bayyana cewa be yadda da kasantuwar Allah ba yayi hira da kafar watsa labarai ta Aljazeera inda ya bayyana cewa ya jagoranci kafa wasu kungiyoyi guda 3 a kasarnan da zasu taimakawa mutane wanda basu yadda da Allah ba su hadu dan samawa kansu mafita.

Mubarak ya gayawa Aljazeera cewa a lokacin da ya gayawa babanshi cewa be yadda da kasantuwar Allah ba sai aka kaishi asibitin mahaukata kuma likitan ya rika gayamai cewa kowa na bukatar Allah, aka kuma bashi maganin da babanshi ya rika tursasamai sai ya sha.

Aljazerar ta yi hira da mutane da dama wanda suma basu yadda da akwai Allah ba a jihohin Kano, Kaduna da babban birnin tarayya, Abuja.

Mubarak ya bayyana cewa tun bayan da labarinshi ya bayyana ya rika samun kiraye-kiraye da kuma sakonni daga mutane daban-daban da suke ce mai suma basu yadda akwai Allah ba amma suna tsoron fitowa su bayyana saboda yanda mutanen Najeriya suka dauki addini da muhimmanci.

Aljazeerar tace Mubarak ne kawai ya yadda aka bayyana sunanshi cikin wadanda ta yi hira dasu amma sauran duk sun bukaci a sakayasu saboda gudun kada su shiga matsala, akwai wanda yace shi dan babban basarakene kuma baban nashi da ya gano cewa be yadda da Allah ba yace mai kada ya gayawa kowa.

Haka shima wani da aka yi hirar dashi yace shi dan babban malamin addinin musuluncine kuma baban nashi yana so ya gajeshi amma shi be yadda akwai Allah ba, yace baban nashi har yankashi da wuka yaso yayi kuma ya koreshi daga gidanshi sannan 'yan uwa duk suka rabashi da 'ya'yansu dan kada ya gurbata musu tunani.

Haka kuma akwai kiristoci wanda suma suka bayyana cewa basu yadda akwai yesu ba da aka yi hirar dasu.

Post a Comment

 
Top