Bayan labarin dakatar da dan takarar gwamnan Kano, Abba K. Yusuf da kotu tayi, me baiwa gwamnan Kanon shawara akan kafafen watsa labarai, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa, tun kamin ranar Asabar, Kwankwasiyya ta mutu kuma an binneta.

Salihu ya kara da yiwa gwamna Me ci, Abdullahi Umar Ganduje murnar lashe zabe.

Ya kuma kara da cewa ya samu rahoton dake cewa, Kwankwasiyyar ta kori Alhaji Ibrahim Al-amin Little wanda shine ya kaita kotu Har ya jawo mata soke zaben ta na fidda gwani.


Post a Comment

 
Top