Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta fitar da wani sako daya dauki hankulan mutane sosai, sakon dai da alama ta yishine akan ko dai wani aboki ko kuma saurayi da suka rabu, kuma da alama cikin fushi ta rubutashi, a cikin sakon dai tana cewa" Duniya makarantace, kullun mutum na kara gogeewa idan yana harka da 'yan iska".

Karanta Wannan: "Wannan tsiraici yayi yawa": wani ya gayawa Sa'adiya Kabala akan wadannan hotunan

Gadai cikakken abinda ta fada:

"Duniya makaranta ,kullum mutum yana sake gogewa in yana harka da yan iska bawai ina nufin shima yana gogewa ya zama dan iska ba,ina nufin yana goge wa ya sake fahimtar halin mutane.Allah duk Wanda kasan ba alkairi bane a rayuwarmu to Allah ka mana katangan karfe da ko waye kuma ko dan waye in kuma mun Riga mun sanshi ne to Allah ka raba dangantakarmu dashi dan hanyar jirgi daban na mota daban .

Dan na fahimci harka da wasu wallahi ba komai yake jawa mutum ba illah bacin suna da bata lokaci da kuma bacin rai da kai nake karfa kasan kanka.harka da kai masifa rabuwa da kai alkairi.tauraro mai wutsiya kenan alhamdulillah yanzu kullum ina cikin farin ciki dan na yadda kwallon mongoro na huta da kuda sarkin kwadayi na kuma rabu da bera sarkin sata.".

©HTDL

Post a Comment

 
Top