Kylie Jenner ta zamo matashiyar da ta fi tsararrakinta arziki a duniya, a cewar Mujallar Forbes a jerin sunayen masu arziki da ta fitar.

Matashiyar, 'yar zuri'ar fitattun iyalan nan na Kardashian, ta samu arzikinta sakamakon sayar da kayan kwalliya da take yi.

Duba Wannan: DA DUMINTA AUDIO: Sabuwar wakar Rarara - Matan Kaduna Dodar

Matsahiyar mai shekara 21, tana da kamfanin samar da kayan kwalliya na Kylie Cosmetics, kasuwancin da ta fara shekara uku da suka gabata, wanda a shekarar da ta gabata kadai ta yi cinikin dala miliyan 360.

Ta kai wannan matsayi ne a shekarun da ba su kai na shugaban Facebook Mark Zuckerberg ba, wanda ya zama biloniya yana dan shekara 23.

"Ban tsammaci komai ba. Ban hango hakan zai faru a gaba ba.

"Amma na ji dadin karramawar. Wannan kara min azama ne aka yi," kamar yadda Ms Jenner ta shaida wa Forbes.

Karanta Wannan: ku kuke jawowa ana ce muku matan banza - wani ya gayawa A'isha akan wannan hoton

TJerin sunayen ya nuna cewa shugaban Amazon, Jeff Bezos, har yanzu shi ne wanda ya fi kowa kudi a duniya.

Jumullar arzikinsa ya kai dala biliyan 131, a cewar Forbes, wato ya karu da dala biliyan 19 daga 2018.

Arzikin Mark Zuckerberg na daga cikin wadanda ke raguwa.

Arzikinsa ya ragu da dala biliyan 8.7 a shekarar da ta gabata, inda ya koma dala biliyan 62.3 a cewar Forbes.

Karanta Wannan: Buhari Kaci zaben 2019 ne da magudi - Inji shugaban kasar Amirka

Sai da aka zo matakin da hannayen jarinsa a Facebook suka fadi da kashi daya bisa uku a lokacin da kamfanin ya shiga rikicin batun tsare sirrin mabiyansa.

Hannayen jarin kamfanin Amazon kuwa sun samu tagomashi sosai sai dai bambancin arzikinsa da na Bill Gates a yanzu ba wani mai yawa ba ne, duk da cewa arzikin Mista Gates din ya karu da dala biliyan 96.5 daga dala biliyan 90 na baya.

A dukkan jerin sunayen masu kudin duniyar, 252 ne kawai mata, kuma matar da ta fi arziki ita ce wata 'yar China mai dillancin gidaje Wu Yajun, wacce arzikinta ya kai dala biliyan 9.4.

Yawan matan da suka fi arziki ya karu zuwa 72 a karon farko cikin shekara 56 da suka gabata.
BBChausa.

Post a Comment

 
Top