![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEj00YZoK1iHyx-99snytb3_Wf_ZFLoqMXgPDEIdXxO6LEWTBN6FpYviynbgBInlbtj7p34edAH-D5XJvYAYqDFIJKjQqei6iWRM8ydgli8fhxmpnKeg_TOojgmanhhS_7vgWrZY0hFv4Bow/s1600/ic-9252.jpg)
Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee wadda tana daya daga cikin na gaba-gaba wajan tallata dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP da yayi rashin nasara a zaben shugaban kasar da ya gabata, Atiku Abubakar, ta dawo daga jiyyar da ta yi bayan kwanaki biyu ba'a ji ta ba a shafinta na Instagram.
Karanta Wannan: Duk Wanda Yafadi Shekaruna Da Ranar Da Aka Haifeni Zan Bashi Dubu Dari - Inji Ummi Zeezee
Ummi ta bayyana cewa maganar siyasa ta wuce tunda shugaba Buhari ya ci zabe, saidai wata ta ce mata bata wuce ba tunda za'a hadu a kotu.
Ummi ta amsa da cewa tabbas hakane dan ba zasu ji dadin mulkinnan na shekaru hudu da ya rage musu ba dan a gantalin zuwa kotu zai kare.
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjQLevvZw418dSUsFGYlGU8K4wCbBCqN7Q4INxUplz4KFbGVd0irze8Smr3K-G2egYiFfysU6T3BrZI2liPv7Ia5nhDP_K8bMKXNKhdlvsak7aNZamvqEFXDk1qToFPrUkZj3zn_2noPE8c/s1600/ic-1857.jpg)
Post a Comment