Amina Muhammad wadda aka fi sani da Amina Amal jarumar fina-finan Hausa ce da ta bar kasar Kamaru zuwa Najeriya don ta ga jarumi Adam A. Zango, don kuma ta fara yin fim, a tattaunawar da jarumar ta yi da Aminiya, ta bayyana dalilin da ya sa ta fara harkar fim, matsalolin da ta fuskanta, nasarorin da ta cim ma, soyayyarta da Adam A. Zango da kuma yadda aka kusa kashe ta a Kasuwar Bacci a Kaduna.
Jarumar ta kuma bayyana cewa za ta iya sadaukar da rayuwarta don jarumi Adam A. Zango. Ga yadda hirar ta kasance:
Daga farko za mu fara da jin takaitaccen tarihinki
Assalamu alaikum, sunana Amina Muhammad, wacce aka fi sani da Amina Amal, an haife ni ne a kasar Kamaru, a can na girma na kuma yi karatu. An haife ni a Bamenda, Shiyyar Arewa maso Yammacin Kamaru ne, amma na girma a Douala, babba birnin kasar Kamaru. Na yi makarantar GSS a Arewa maso Yammacin Kamaru, sannan na yi sakandare ta GBS a Douala.
Ga shi an haife ki a Kamaru, kin kuma girma hade da karatu a Kamaru, sai kuma ga ki a Najeriya, shin da ma kina da wadansu ’yan uwa ne a nan Najeriya?
Ba zan ce ba ni da ’yan uwa a Najeriya ba, amma dai inda na je a Najeriya ba ni da ’yan uwa, duk da cewa ina da ’yan uwa a Najeriya, amma a Yola suke da zama, amma lokacin da na zo Najeriya a jihar da na zauna ba ni da ’yan uwa.
Mene ne ya yi sanadiyyar zuwanki Najeriya har ta kai ga kin sauka a wurin da ba ki da ’yan uwa?
A lokacin da nake Kamaru wata rana sai na je dakin wata makwabciyata sai na ga tana kallon fim din Hausa, ba na kallon fina-finan Hausa a lokacin, amma sai na zauna na kalli fim din, zan iya tunawa sunan fim din ‘Hubbi’, bayan na gama kallon fim din sai na fara sha’awar in yi fim, na rika cewa ina ma ni ce jarumar cikin fim din, sai na fara tambayar kaina ta yaya zan yi fim a Kamaru, tun da ba a yin fim din Hausa a can, a zahirin gaskiya jarumin fim din ya burge ni sosai, na ce ina ma a ce wata rana in fito fim tare da shi, daga lokacin sai na fara sha’awar zama jaruma.
Wani jarumi ne ke nan?
Ba kowa ba ne illa Adam A Zango.
Kin ce ba kya kallon fim din Hausa sai a kan ‘Hubbi’ kika fara, to ta yaya Zango ya zama miki jarumin da kika fi so?
E, to kamar yadda ka sani, ka san Adam A Zango mawaki ne, duk da ba na kallon fim din Hausa ina jin wakokinsa, kuma abin da ya sa nake jin wakokinsa shi ne, suna yi mini dadi, sannan yana sa Turanci a ciki, sannan ka san Kamaru ba wai Turanci muke yi ba, amma dai akwai mutane da yawa masu jin Turanci, don haka idan ya yi Turanci sai abin ya rika yi mini dadi.
Yaya aka yi kika yanke shawarar zuwa Najeriya?
Ranar da muka kammala kallon fim din ‘Hubbi’ a ranar da na koma dakina a cikin dare dai ban yi barci ba, ina ta nazari, domin ban san ta yaya zan bullo wa iyayena ba, hakan ya sa abin ya rika damu na, idan na kwanta da rana sai in rika mafarkin ina aktin, da daddare ma haka, kullum dai ina cikin mafarkin ina aktin, sai abin ya fi karfina sai na samu mahaifiyata na yi mata bayani, sai ta ce mini ko na fara hauka ne, idan na fara kuma in fada musu su kai ni asibiti, na ce mata ban fara hauka ba, na dai yi musu bayani, amma dai ba su ba ni goyon baya ba.
Abin dai ya fi karfina ya zamanto ko hira nake yi da mahaifina to ina yi masa hirar Adam A. Zango a ciki, haka ma dai mahaifiyita, abin dai ya fi karfina har ya zama kamar zan yi hauka, to ka san babu iyayen da za su so a ce ’yarsu ta haukace saboda wani burinta na rayuwa. Bayan sun zauna sun yi magana sai suka ce mini, tun da abin da nake so ke nan to sun bar ni in zo Najeriya in yi.
Daga nan sai kika shirya kika taho Najeriya ke nan?
Bayan sun amince mini sai aka fara samun cee-kuce a cikin danginmu, sai bayan kusan kamar wata biyu na zo Najeriya, dalili kuwa shi ne abin ya haifar da cece-kuce a wurin dangi, bayan sun kammala tantancewa kuma na yi musu alkawarin ba zan aikata duk wani mummuna abu ba, domin sun san tarbiyyar da suka ba ni, don haka idan har sun ba ni yardarsu to kada su ji komai, na kuma yi alkawarin zan rike musu amana, hakan ya sa suka sake amince mini in taho Najeriya, suka ba ni guzuri mai yawa da zai rike ni zuwa wani lokaci mai tsawo, sai na taho Najeriya.
Bayan zuwanki Najeriya ina kika nufa, kuma yaya rayuwarki ta kasance?
Abin ba a cewa komai, kai ma ka yi tunanin mutum ya je wurin da ba shi da kowa, ba shi da dangin uwa bare na uba, ga shi ma ban ma iya Hausa ba, na samu matsala sosai, a haka dai na rika rayuwa.
Daga farko dai na sauka a Abuja, sai na ce a kawo ni KD, kasancewar a lokacin nakan ji Zango yana ambaton KD a cikin wakokinsa, bayan na duba a intanet sai na fahimci KD na nufin Kaduna ke nan, sai na ce a kawo ni Kaduna, kuma a nan na sauka.
A cikin bayaninki kin ce lokacin da kika zo Najeriya ba kya jin Hausa, to da wane yare kika yi amfani da kika zo Najeriya har kika zo Kaduna?
Ka san ta Arewacin Kamaru an fi yin Hausa, duk da dai ina dan jin Turanci, to a Najeriya wani lokaci ko na hadu da Hausawa in na yi musu Turanci ba ji suke yi ba, sai mu rika yin na bebe, to a haka na rika fahimtar mutane, a wani wuri ko ina so in yi magana ma sai in fasa, su kuma idan sun yi Hausa ba zan ji ba.
A kasar Kamaru da ma can kina jin Turanci ke nan?
A’a, a wurin da na tashi dai Faransanci ake yi, kuma makarantar da na yi duka da Faransanci aka koyar da ni, amma daga lokacin da na fara tunanin in zo Najeriya sai na tafi wata makaranta a Kamaru da ake kira Linguistic Centre, sai na yi rijista, sai ya zamo idan na dawo daga makarantar boko da rana, idan yamma ta yi sai in tafi makarantar koyon harsuna, kuma ana ba ni darasin awa biyu ne kowace ranar da na je daukar darasi, a cibiyar ana koyar da duk wani yare na duniya, amma sai na zabi Turanci saboda bayan na yi bincike na gano cewa Turanci shi ne yaren da ake amfani da shi, sai na ce bari in koyi Turanci, kuma a lokacin na ji an ce Hausar Najeriya ita ce gangariya a cikin duka Hausar da ake yi a duniya shi ya sa na ce ba zan koyi Hausa a Kamaru ba, na ce idan na zo Najeriya na koyi Hausa a nan.
Bayan kin zo Najeriya kin dauki tsawon wani lokaci kafin kika hadu da Zango?
Na yi wata biyu zuwa uku kafin in hadu da Adam A. Zango.
Me ya faru a ranar da kika fara haduwa da Zango?
Ranar da na fara haduwa da Zango na yi farin ciki sosai, a ranar da muka hadu wanda ya hada ni da shi ya buga mini waya ya ce in shirya zan hadu da Zango yau, bayan na shirya sai ya zo muka je wurin da Zango yake, to ina sauka sai aka ce in zo in gaishe shi, na je na same shi, sai na ce kai ne Adam A. Zango?
Sai ya ce ba ga ni nan kina kallona ba? Sai na duba hotonsa da ke kan wayata, sannan na kalle shi, sai na ce anya kai ne kuwa?
Sai ya ce wallahi ni ne, sai na ce masa to shi ke nan, sannan na ce masa na zo daga Kamaru don in yi Hausa fim, kuma kai ne dalilin zuwana Najeriya, na ce kuma ni babbar masoyiyarsa ce, sai ya fashe da dariya, ya ce ta yaya za ki yi fim bayan ba kya jin Hausa?
sai na ce masa, idan har ya yi mini alkawarin zai yi mini fim, to na yi masa alkawarin zan koyi Hausa, sai ya ce to shi ke nan, sai na ce masa ya ba ni wata biyar sai ya ce mini to ya ba ni shekara daya, sai na ce masa to shi ke nan.
To, a wata nawa kika koyi Hausa?
A cikin wata biyar na koyi Hausa, amma a lokacin idan na yi magana sai kowa ya yi dariya, duk da cewa har zuwa yanzu ban kware sosai ba.
Wadanne matsaloli kika fuskanta a lokacin da kike koyar Hausa?
Na dan fuskanci wadansu matsaloli, kodayake ta wani bangaren zan iya cewa ba matsala ba ce, saboda idan zan yi magana zan iya in zagin mutum, a wurina kawai kalmar ta yi mini dadi ne, kai kuma za ka ga kamar zagi ne, amma a wurina ba haka ba ne, sannan idan na je wurin mutane zan ga ana ta magana ni sai in zauna in rika kallon su, amma ba na iya magana, ko ana cinikin sayar da ni ne ma ban sani ba.
Bayan duka wadannan abubuwa sun faru, to yaya kika ji da aka ce za ki fara fitowa a fim?
Fim dina na farko shi ne ‘Amal’, kafin in yi ‘Amal’ an ba ni labarin fim din, inda ya yi kamar wata shida a hannuna, domin sun san ba na jin Hausa sosai, amma sun san ina karatun Hausa, sai suka ba ni (script) suka ce in rika karantawa ina gwaji (rehearsals) a gida. A ranar da aka ba ni (script) din ban ma iya barci ba, saboda murnar cewa burina ya kusa cika, haka na rike (script) har tsawon wata shida, in fada maka a takaice dai na haddace fiye da rabin (script) din, idan an zo wuri ba sai an fada mini ba, domin na san abin da aka rubuta a wurin.
Za mu ci gaba mako mai zuwa.
Post a Comment