Wani saurayi ne ya je zance, sai budurwarsa ta nemi ya bata labari, sai ya ce toh amma labarin part 1, 2, 3, da 4, sai tace ya bata, saurayin ya fara kamar haka;

part 1: Wani miji ne da matarsa, suna cikin tafiya a mota, can sai suka zo mararrabar hanya, sai yacewa matar wace hanya zamu bi ?

matar tace a’a dai maigida mubi hanyar da ta bi dama, aikuwa sai ya kwashe ta da mari yace nina ke tuka motar ko kuwa ke? hanyar hagu za mu bi, sai budurwar ta saka dariya tace amma wannan miji akwai mugu, saurayi yace saura

Part 2: suka bi hanya suna tafiya suka iso gun masu sai da kifi, maigida ya siya musu, matar tace maigida mai xa’ai da shi, ya ce dafawa zakiyi, aikuwa matar ta zabge shi da mari, tace kaike girkin ko ni?? Soyawa zanyi,

Budurwar ta kyalkyale da dariya, ta ce amma ta burgeni ka ga sunyi duro, saurayi yace saura

Part 4, sai budurwar tace a’a.

Part 3 dai, saurayi ya kwasheta da mari, yace ni nake bada labarin ko ke…!! Toh wai idan kaine/ke ce budurwar, me zaki yiwa wannan saurayin??

Post a Comment

 
Top