Yadda ake kwanciyar da mace ka fin a sanyata fim.

Mutane da dama dai ba tun yau ba suna kokawa da yadda masana'antar fim din Hausa ta Kannywood ke gurbata tarbiyya da al'adun malam Bahaushe.

Baya ga haka ma dai wasu na yiwa yan fim din kallon wasu bata gari inda ake yi wa da yawa daga cikin matan kallon wadanda ke sai da budurcin su a farfajiyar masana'antar ta fim. Wasu ma suna yi wa duk wata 'yar fim kallon karuwa.

Lamarin da yasa wasu daga cikin mutane su ke tsoron su bar 'yan uwan su mata shiga harkar fim.
Mutane da dama rashin adalci da rashin sanin hakkin Dan Adam ke sanyasu kalaman tozarci ga masana'antar fina-finan Hausa.

A iya bincikena Babu wata masana'anta ta shirya fina-finai a duniya da 'yan uwan su suke tsangwamar su, suke kyamar su kamar al'ummar Kasar Hausa da suka tsani 'yan Kannywood, wadda har yanzu babu wata hujja da mutane dogara da ita na tsanar jaruman fina-finan Hausa.

'Yan Hausa fim mutane ne kamar kowa kuma ba mu ce ba su yin kuskure ba, amma irin kiyayyar da ake nuna masu ta yi yawa.

Karanta Wannan: Na Yi Da Na Sanin Soyayyata Da Timaya - Ummi ZeeZee

Sannan akan masu cewa 'yan fim din Hausa na bata tarbiyyar yara, wannan sha-ci fadi ne kawai domin ita tarbiyya daga gida ta ke tashi. Tun kafin bullowar fina-finan Hausa, a Kasar Hausa akwai gidan karuwai, gidan shan giya, mu na da 'yan daudu, da kuma 'yan luwadi, wadanda dama can ana yin wadannan abubuwan na alfasha tun fil-azal.

Ku kuna nufin ba mu bin tarihi?

Me yasa ba ku taba fadin alherin su ba sai sharri. Ko kun manta da cewa ta sanadiyyar fim daya da jarumi Adam A Zango ya shirya mai suna 'Ahlul Kitab' mutane bakwai suka musulunta, shin akwai wata kungiya ko wani mutum Wanda ya karrama shi ta dalilin wannan gudummuwa da ya ba addinin musulunci domin ya kara masa kwarin gwiwa, idan akwai muna sauraro sai ku fadi.

Da yawa daga cikin mutanen da ke aibata masu sana'ar fim dukkan su babu wanda ba zai rantsewa da alkur'ani akan cewa bai taba kuskure ba. Da za a bi kadin rayuwar wani ta sati daya ina mai tabbaccin gwara ma rayuwar 'yan fim din da tashi.

Wani shirka ya ke, wani luwadi ya ke, wani mazinaci ne, wani Barawo ne, wani giya ya ke sha. da sauran su. Amma ba su duba rayuwar su ko rayuwar na kusa da su sai rayuwar 'yan fim wadanda ke sana'a.

Irin wadannan mutanen ma su zagin 'yan fim idan ka je a gidajen su, su ne za ka tarar da tashohin arna da turawa wadanda ake kallon fina-finan turanci a tashohin. A fina-finan da suke kallo a gidan su babu irin iskancin da ba a nunawa, ana rungumar mata a ciki, bugu da kari a sadu da su, uwa uba ga shigar tsiraici a cikin fina-finan amma babu wanda aka ji ya fito ya soki wadancan fina-finan sai na Hausa da aka raina.

Shiyasa yanzu sharrin na su ya kai har ana yamadidin cewa wai sai an kwanta da mace kafin a sanyata a cikin fina-finan Hausa.

Irin wadannan labaran da wasu gurbatattun kafafen sadarwa ke rubutawa social media, su na rubutawa ne kawai don son ran su, domin babu wata kwakkwarar hujja da za su kare kan su a gaban ubangiji na cewa sai an yi amfani da mace kafin ta shiga fim.

Karanta Wannan: Karuwai Da 'Yan Kwaya Suna Girmamani - Inji Hauwa Waraka

Hasalima babu wata shahararriyar 'yar fim wadda ta fito duniya ta taba cewa an yi amfani da ita kafin a sanyata cikin fim.

Kawai wa su ne ke zaunawa su kirkiro sharri da karya don su ga sun batawa masana'antar fim suna, to sai dai kun makara domin Bakin Alkami ya bushe. Sannan Zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana mazuru ana shaho sai ya yi.

Ba zan ce ku daina fadin sai an kwanta da mace sannan a sanyata a fim ba, ba zan hanaku zagin 'yan fim tare da aibatasu ba, sai da zan ce ku tanaji hujjojin da za ku kare kan ku a gaban ubangiji a ranar da kowa ya ke ta kan shi. Domin shi Allah bai barin hakkin wani kan wani.

Mata 'yan wasan Hausa ba karuwai ba ne, idan kuma ka ce karuwai ne, saboda suna cudanya da maza a wurin aiki, To fa duk wata daliba ko ma'aikaciya ko 'yar kasuwa da ta kama gida ta zauna ko kuma ta ke hudda da maza a wurin aiki sunanta Karuwa kenan..

Isah Bawa Doro

Post a Comment

 
Top