Dan takarar shugabancin Najeriya na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya kaddamar da tawagar lauyoyin da za su kalubalanci sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabarairu da shugba Muhammadu Buhari ya lashe.

Tawagar lauyoyin, na karkashin jagorancin Dr Livy Uzoukwu SAN, wadda za ta garzaya kotun sauraron kararrakin zabuka, da bukatar bada umarnin sake sabon zaben na shugaban kasa, ko kuma bayyana Atiku Abubakar a matsayin wanda yayi nasarar lashe na makon jiya.

A Larabar da ta gabata, hukumar shirya zaben Najeriya INEC, ta bayyana shugaban kasar Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin Najeriyar karo na 2, da yawan kuri’u miliyan 15 da dubu 191, yayin da Atiku Abubakar ya samu kuri’u miliyan 11, da dubu 262, da 978.

Sai dai kwana guda bayan haka, dan takarar na PDP ya yi watsi da sakamakon, bisa zargin tafka magudi a cikinsa, sai kuma amfani da sojoji, wajen cin zarafi jama'a da hanasu kada kuri’a a jihohin da jam’iyyar ta PDP ke da mafi rinjayen magoya baya.

RFIhausa.

Post a Comment

 
Top