![](https://www.alummata.com/wp-content/uploads/2019/03/mad.jpg)
Wani Malamin Makarantar Islamiyya mai suna Malam Hashiru Bala da ke cikin garin Jalingo a jihar Taraba ya yi sanadiyyar ajalin dalibinsa bayan da ya murde masa wuya har lahira.
Dalibin mai suna Mohammed Sudais mai shekaru 9 da haihuwa dan wani hamshakin dan kasuwa ne da ke zaune a garin Jalingo.
![](https://www.alummata.com/wp-content/uploads/2019/03/Sudais-da-mahaifinsa-300x150.jpg)
An fara neman Sudais ne a ranar Lahadin da ta gabata bayan ya fita sallar Magariba kuma rashin jin duriyar sa yasa iyayensa suka bazama nemansa inda a sakamakon haka ne wani abokin Sudais ya fadawa iyayen yadda Malamin Islamiyyarsu Malam Hashiru ya yi ta masa wasu tambayoyi da bincike kan inda Sudais ke zuwa kafin bacewarsa.
©Alummata
Post a Comment