SIRRIN GANE MACE TA GARI

A mataki na farko na samun nagartacciyar mace shi ne, ka zama nagari. Matukar ka zama nagari, to ana sa ran za ka samu mace tagari. 

A dabi’ar kowane mutum yana burin aurar mace tagari ko da shi ba nagari ba ne, domin kowa ya tabbatar da cewa mace tagari babbar alheri ce ga mijinta.

Akwai bukatar idan ka tashi neman aure, to ka tsaya ka yi zurfin tunani a kan wacce za ka aura, ka natsu ba a son gaggawa, kada ka biye kyale-kyalen duniya, ko wata karairaya da mace za ta yi maka, kada ka rudu da cewa mahaifinta mai hannu da shuni ne.

Ya dan uwa akwai bukatar ka lura da wadannan alamomin mace tagari kafin aure da suka hada da: ana so ta kasance mai tarbiyya, mai ilimi da aiki da shi, mai natsuwa da kamewa, ta kasance mai lizimtar addini, ta kuma kasance mai kunya.
Bayan an yi aure kuwa: ga alamomin da ya kamata ka duba kamar haka: Rashin yi wa miji gori, godiya da dawainiyar da yake yi mata, rashin kushe kokarinsa, rashin dora masa dawainiya da wahalhalu na babu gaira babu dalili. Sauran sun hada da yi wa miji biyayya karfafa shi a kan irin kokarin da yake yi, neman shawararsa a kan al’amuranki, rashin cutar da shi, girmama iyaye da ‘yan uwansa,
Haka babu laifi ka duba mace mai kyawu, ma’ana ka ce kai mai kyau za ka aura kana da damar yin haka, ba laifi ba ne, amma Musulunci ya hana aurar mace don zallar kyawunta ko yawan dukiyarta, inda Ma’aiki SAW ya ce: “Kada ku auri mace don zallar kyawunta ko dukiyarta ko nasabarta, ku dai ku auri ma’abociyar addini hannunka zai ribatu”
Wani kuma ya fi son baka, wankan tarwada, wani kuma shi duk yadda za a yi ya fi son fara kamar yadda a zamanin nan mutane da yawa suke raja’a a kai. Idan har ka samu duk wacce kake so din, to lallai kada ka sanya yaudara a ciki, yi kokari, ka gaya mata gaskiyar halin da kake ciki, ita ma ta gaya maka gaskiya, kada ka bari ta yaudare ka, kuma kai ma kada ka yaudare ta.


Lallai ka more! Kuma abin a yi maka murna ne samun mace tagari, domin duk wani dadin duniya da mace tagari ne yake tabbata, kuma matukar aka samu uwa tagari, to babu shakka za a samu ’ya’ya nagari, kasa kuma sai ta zauna lafiya, kwanciyar hankali da wadata su yalwata.

 

Mace ta gari za a same ta da: *.

KAMEWA: Daga duk wani abu da zai sosa wa maigidan ta rai, a kanta ne ko gidansa ko abincinsa da sauransu

GASKIYA: In za ta yi magana ba ta qarya, domin samun riqe gidan gaba daya.

AMINCEWA: Duk abin da yake so ta yi ta amince, don yarda da cewa ba zai halakar da ita ba, tana qaunarsa.

TAWALU'U: Ta qanqar da kai gare shi koda kuwa tana da ilimi, arziqi da shekaru sama da shi, kamar dai Khadeejah R.A da Annabi (S.A.W)

NATSUWA: Kar ta riqa tuno abubuwan da suka gabata, kuma ta dena tsoron masu zuwa.* *. KUNYA: Ta riqa jin kunya, wannan ado ne gare ta, masamman in tana tare da mijinta a cikin jama'a, wannan zai qara masa qaunarta

KWANCIYAR HANKALI: Mantawa da matsalolin rayuwa da qoqarin tura farin ciki ga mai gida koda suna cikin matsala.

GODIYA: Duk abin da ya zo da shi a nuna masa jin dadin zuwa da shi komai girmansa komai qanqantarsa.* HAQURI: A kan duk abin da zai bayyana daga miji (wannan ne kawai muka dauka alhali suna da yawa)* *.

TSAYUWA QYAM: A wajen bauta da qarfafa mijin da 'yayan su.

 

SANNAN TA KASANCE MAI

1. AMANA: Ta zama mai amana, kar ta yarda maigidan ta ya ga ha'incinta koda kuwa sau Daya ne, ta riqa gaya masa abin da za ta yi domin maganin shedan

2. CIKA ALQAWARI: Yana Daya daga adon mace da namiji.

3. TSORON ALLAH: A duk abin da za ta yi.

4. DANNE ZUCIYA: Yayin da aka baqanta mata rai.* Wadannan abubuwa guda 14 su suke nuna mace nagari, dan uwana kada ka riqa binciken qyalqyal banza, ke ma yar uwa ki dai na kallon kudi ki duba rayuwarki idan kin shiga gidansa, komai kudinsa in ba kwanciyar hankali ba za ki ji dadinsu ba. Biyayya ga miji ba mai iya wa sai mace ta tagari,da yawa mata suna so a ce su ne wadan da Annabi (S.A.W) ya sifanta dinnan da (Nagari) sai dai biyayyar ce ta yi qaranci, ko za a yi sai dai a gabansa in ya matsa an watsar kenan. Mace ta gari takan yi qoqarin ta zama wa mijinta aljannarsa ce, ba ta son ta ga gazawarta a idanunsa, don haka takan yi farin ciki in taga murmushinsa, takan damu matuqa in ta ga fushinsa ko da ba da ita yake ba, ba ta jinkiri a wajen abinci, kuma ta iya dafawa ba tare da almubazzaranci ba, ita ce amin taccen abokin shawararsa,mai iya riqe masa sirri, ba ta yarda wani ya sani ko waye kuwa, sannan ga taimako.

SIFFOFI 12 NA MACE TAGARI

1. Mace tagari ita ce wacce Idan Mijinta ya kalleta Zai ji farin ciki ya lullubeshi.

2. Ita ce wacce take gaggawa wajen cika umurnin Mijinta.

3. Ita ce wacce take mutukar kiyaye duk abinda zai ‘bata ma Mijinta rai.

4. Ita ce wacce take dagewa wajen bautar Ubangijinta.

5. Ita ce wacce bata wasa da duk wani Hakki na mijinta.

6. Ita ce wacce duk lokacin da Mijinta yayi fushi, batta samun kwanciyar hankali har sai ta yardar dashi.

7. Ita ce wacce take Kiyaye Duk wani sirrin Mijinta.

8. Ita ce wacce idan Mijinta ba yanan take Kiyaye mutuncin Kanta, da kuma dukiyar da ya bari agida.

9. Ita ce Wacce take kulawa da Tarbiyyan Mijinta da ‘ya’yansa koda ba ita ce ta haifesu ba..

10. Ita ce wacce take mutukar girmama Iyayen Mijinta kamar yadda take girmama nata iyayen.. Kuma take kyautatawa ‘yan uwansa ba tare da tsangwama ba.

11. Ita ce wacce take zama da Makobtanta da kishiyoyinta cikin tsoron Allah da kyautatawa. Koda su suna munana mata..

Ya Ubangiji Ka Azurtamu Da Mataye Nagari,Da ‘Ya’Ya Nagari Da Dukiya Me Albarka !!! Ameen

 

Wadanne Hanyoyin Za Ki Bi Namiji Ya Aure Ki

Maza su kan zama a rude yayin da su ka tashi neman mace tagari har su kan shiga shakka kan wace ce macen da ya dace su aura. Amsar da su ke samu ita ce, su yi duk inda za su yi su lalubi mai kamun kai, domin daga ita ne a ke samun mace tagari. Ita kuwa mai kamun kai siffofinta a bayyane ya ke, inda namiji in ka kura ido ka tsanannta nema, to za a dace. Mace tagari ita macen da Bahaushe ke kira mai kamun kai wadda ta siffantu da kakkyawar dabi’a da halaye da kamala, wacce kuma kallo daya za a iya gane tarbiyyarta da kokarin da iyayenta su ka yi wajen ba ta tarbiyya. Mace ta kwarai ita ce wadda kowanne namiji mai hankali zai yi fatan a ce ta na gidansa ta zame masa sanyin idaniya ta zama al-mar’atissaliha da Annabi Muhammad (SAW) ya ce ta fi duniya da duk abin da ya ke cikinta. Mace ingantacciya ita ce dai matar da kowanne namiji zai so ya sami zuriya da ita. Mata da dama da za ka tattauna da su shi ne babbar matsalarsu mijin aure, abin haushi da ke damun su ga masoyan nan kamar jamfa a Jos, amma auren ya gagara. Mata na ta wahala addu’a da ’yan dabaru kana su na ta fama, amma abu ya ki yi wuwa. Tashin hankalin ba ga matan ba zawarawan ba. Mace wadda ba ta da makusa ta kowanne bangare kyau ko asali ko ilimi, amma aure ya gagara a na ta laluben dalili an kasa gano gaskiya abu guda ke zagayawa a kwakwalwarsu shi ne maza mayaudara ne, amma fa duk yaudararsu su na neman mace tagari ne, don sa wa a daki.

Kamun kai Idan ka tashi neman matar da za ka aura ka dage ka nemi mai kamun kai. Ya na cikin matakin farko da mace ya kamata ta fara nunawa a gun duk wanda ta ke so su kulla mu’amala da ta ke fatan dorewarta zuwa aure. Hanyoyi da dama za ka lura da shi in ka na son gane mace mai kamun kai, kada ka jira a ba ka labari; kai da kanka za ka sa ido ka lura. Mata a yau a tunaninsu yadda su ke ganin maza na haba-haba da mata ba tare da nuna wani zabe ba, to su sani iyakarta waje ne.

Sutura Sutura ita ce abin da a ke sanyawa a jiki don kare tsiraici. A sutura a na gane kamalar mutum. Abu na farko da kan ja hankalin namiji ga mace har ya gane ajin da zai ajiye tashi ne irin suturar da ta saka jikinta. Mata a yau su na tunanin bayyana tsiraicinsu shi ne hanyar da za su iya janyo hankalin namiji gare su har ya gane kyan wani bangare na jikinsu da zai kai su ga aure. Wannan kuskure ne, domin namjin da wannan zai dauki hankalinsa har ya yi tunanin ku yi sabo, to tabbas sai dai soyayya, wanda a karshe danasani ne zai biyo bayan haduwar. Ya na da kyau mace ta yarda da cewa mijinta duk inda ya ke zai tarar da ita, sannan ba wani dace da za a samu a sabon Allah.

 

Surutu barkatai alamu ne na rashin kamun kai. Macen kwarai ba a san ta da daga harshe ba ko da a cikin ’yan’uwanta mata ne bare kuma maza. Wata matar ta na tunanin idan ta shiga dandazon maza ta daga muryarta da zakewa shi ne zai janyo hankalin namiji kansu. Mace mai surutu rau-rau a kan titi ko cikin maza ba ta cikin irin matar da ka ke nema ka aura. Mace mai kamewa da karancin magana ko da kuwa a wajen saurayin ne abar yabo ce da soyuwa ko da batun auren ne irin su a ke nema a adana a gida.

Kunya Bahaushe ya ce kunya marin da. Ka tabbatar matar da za ka aura mai kunya ce, don kuwa duk macen tagari an san ta da kunya da yakana da kara. Mace ba ta isa mace abin sha’awa idan har ta zamanto fitsararriya. Akwai hanyoyi da dama da mace za ta nuna kunya kamar haka: Zance barkatai Yin surutu rau-rau kafin namijin ya yi guda kin yi goma. In har aka zo batun aure maza ba irin wannan suke nema ba in har kina neman mijin aure to anan kin fadi jarrabawar.

Ciye-ciye Mata a yau sun zubar da kyakkawar al’adar nan ta kame kai wajen ciye-ciye a kan hanya ko gaban samari. Mace mai ciye-ciye da rashin kimtsi ko ga sa’anninta mata ba ta farin jini bare maza. Duk matar da ka ganta tana ciye ciye kan turba bar ta kawai ba ta shirya samun mijin aure ba.

Roko shi ma wata hanya ce ta nuna rashin kunya da mata kan dauka hanya wayewa. Duk matar da ta fiye roko tana kashe wa kanta wata daraja ne ga mai sonta kuma in har mace ta fiye roko to fa tana nunawa wannan da zai aure ta irin zaman da za su yi. Hali na farko da za su sa a ran su in har suka kai ki gidansu ba za ki iya hakuri da samu da rashi ba sannan duk randa babu ba za ki iya rufa wa zamantakewar asiri ba. Roko ga mace babbar hanya ce ta zubar da mutunci. Don haka in budurwarka ta ishe ka da ba-ni-ba-ni na ba gaira ba dalili to fita a guje ba ba matar aure ce ba

kallo kadai a na iya bayyana halin mace, tarbiyyarta da kunyarta da dacewa ka kai ta gida ko kuma ba za ka kai ta ba. Ka lura da yadda wadda za ka aura ta ke kafe ka da ido, ba rusanawa, to ka bi a sannu

 

Rashin jan aji Mace ta kirki da jan aji da kamewa a ka santa. Ba wai ta zama mai girman kai ba, amma ka nemi wanda ta san darajar kanta. Idan har mace za ta zama arha kowanne namiji ya kira ta ba tantancewa ta je, kowa yake bukatar jin hira ko yawo ita za a zo nema a tafi da an ce ana sonta to fa kasuwa ta bude ba sauran edcuse to fa mai irin wannan halin ta kade ba ta sa dan-ba ba a wajen neman mijin aure ba. Kai ma me neman matar kwarai kada ka leka.

 

LALLE
 
Yar’uwata ki sani lalle kwalliyace ga duk ya mace kuma mace idan ta bar hannunta ko kafarta ba lalle to ba’a iya banbance ta da namiji. Kuma kowace irin kalan lalle da mata sukeyi kema kiyi da zaran ya goge sa ki biyoshi da wani kala domin cika siffarki ta ya mace.
 
BANGAREN ADO
 
Yar uwa ki sani kirkire kirkiren adon zamani wajibine akanki a gidan mijinki harma da irin naki salon adon, kuma duk wata dressing da mata sukeyi a duniya dolene ki rinka yiwa mijinki matukar bai sabawa addinin musulunci ba, sannan kiyi masa ado da duk irin kayan da kika mallaka.
 
KISISINA DA KARERAYA
 
Ya yar’uwata mace bata cika mace ba idan bata iya kisisina irin ta mata ba, kamar su kareraya, yanga da rigima. Kuma ki sani irin wadannan dabi’un su suke daukaka martabar mace a wurin mijinta acikin dukkan alamuran su, Magana ko tafiya ko kallo da makamantansu.
 
DAMUWA DA DAMUWARSA
 
Yar uwa wajibine ki karanci halin mijinki sosai kisan mijinki acikin halin farin ciki da kuma bakin ciki kuma ki lura da yanayin sa a lokuta kamar haka:
 Lokacin fita nema
 Lokacin dawowa daga nema
 Lokacin gajiya
 Lokacin farin ciki
 Lokacin bakin ciki
 
 LOKACIN FITA NEMA: 
 
A wannan lokaci yaruwata ki sani dolene ki tabbata mijinki ya fita daga gida cikin kwanciyan hankali da natsuwa. Akwai wani dabi’a da matan magabata sukeyiwa mazajensu, su kan shirya bayan sunyi wanka da kwalliya sannan sai su raka mazan su har kofar gida ko kofar daki, sannan suna tafiya suna taku daddaya da rangwadi kuma su kan yimusu addu’a sannan su basu wasiyan cewa idan Allah yasa ka samu halal ka kawo mana, idan kuwa baka samu ba zamuyi hakuri da azabar yunwa akan azabar Allah. Bayan ya fita yayi nisa sai ki kirashi da wani sunan soyayya mai dadi sai kiyi masa Kiss da hannunki. Sai kice masa Allah ya bada sa’a. Allah ya sa mudace Ameen.
 
 LOKACIN DAWOWA DAGA NEMA: 
Ki sani yar’uwata miji yana dawowa gida a halin gajiya kafin ya dawo kin shirya ma dawowarsa.
 
 LOKACIN GAJIYA:
A wanna lokaci ki sani zaki nemi ruwa mai dumi a lokacin sanyi idan kuma lokacin zafine, sai kinemo ruwan sanyi ki kai masa wurin wanka bayan ya gama wankan ya dawo daki ki bashi abinci
 
 LOKACIN FARIN CIKI: 
Yar’uwata a wannan lokacine zaki baje kolin shagwabar ki da rungumarsa
 
LOKACIN BAKINCIKI: 
 
Yar’uwata a wannan hali babu wasa babu tsokana a tsakaninku har sai kinji mai ya bata masa rai, idan ya fita bai samo bane sai ki kwantar masa da hankali, sai ki nuna masa kullum Allah yana basa sai kawai don yau baka samo ba sai muyi hakuri mu godewa Allah. Idan kuwa wani ne ya bata masa rai, sai ki bashi hakuri da kuma kwantar masa da hankali, sannan idan ya dawo miki cikin tashin hankali sai ki warware masa bayan kinji mai ya faru dashi. Idan ba zaki iya warware masa ba sai ki kaishi inda za’a warware masa damuwarsa.
 
IYA ABINCHI
 
Rashida wallahi wannan shine babban hanyar sace zuciyar miji idan har kin iya abinci sosai, wallahi sai dai kiji mijinki yana cin abinci yana santi yana kuma cewa amarya Allah ya miki Albarka harma ya miki kyauta sakamakon santin cin abincin. Sannan ba zai taba jin tsoron duk bakon da akayi ba ta bangaren abinci kam ko da kinyi masa laifi sai yace ya yafe saboda santin abincin. 


 


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top