Tun azal, Sabara na daya daga cikin itatuwan da Hausawa ke amfani da ita a fannin maganin gargajiya dan warkarda cututtuka masu dimbin yawa da suka fi dangantawa da ciwon daji kona iska kamar yanda mun ka sani al’adance.
Wasu masana maganin gargajiya dake a yankin Dogo dake a kasar Mali suna daga cikin wadanda suka bankado sirrin sabara ta fannin warkarda ciwon daji da wasu cututtukan dake da na saba da ciwon da Hausawa ke kira iska mai fakewa a cikin jiki yana canza kamannin da zai yi matukar wahala a iya magance shi ta amfani da maganin bature.
Daga bisani sai wani rukunin wasu likitoci daga kasar Faransa suka shigo dan tantance gaskiyar maganin da aka ce sabara na yi, wanda daga karshe sun gano gaskiyar maganar cewa sabara na yakar ciwon daji.domin akwai. A harshen Faransa ana kiran sabara da Guirea du Senegal.
A Lokuta da dama mutum zai hadu da ciwo sai ya je ya yi ta faman bincike da kashe kudi da lokaci mai tsawo ana sayen magani kala-kala na bature ana sha dan warkarda wani ciwo a jiki amma kuma sai ciwon ya gagari maganin daga bisani sai ka ga idan an dawo gana gargajiya, cikin ikon Allah sai a da ce. Dama ciwo da kuma magani fada suke yi da juna, duk wanda ya fi karfin wani to shi zai yi nasara. A sanda ka sha magani za ka iya jin yanayin jikinka ya canza kamar ka rinka jin zafin jiki ko ciwon kai da kasala da tashin zuciya ko ka ji duk baka jin kanka yadda kasa ji to a wannan halin maganin da ka sha ne ya tsakuro maka da ciwon dake a cikin jikinka dan ya fito su fafata duk wanda ya fi karfin wani shi zai mamaye jiki. Idan ka sha magani ka ji ba dadi sai ka yi jifa da shi to shi kenan ciwo ya sami mafuka kenan, amma idan ka daure to za ka ji ciwon na lafawa dan maganin zai ci gaba da kashin wadannan kwayoyin cuta har ya ga sun mutu.
Sai dai kuma ba kowane ciwo ake shawa sabara ba. Akwai hatsari ka sha sabara a sanda baka san ainihin ciwon dake damun ka ba, domin takan iya tado maka da wani abu na daban.
Ga kadan daga cikin amfanin sabara ga jikin dan’adan.
-A kasar Hausa, mata su kan yi amfani da ganyen sabara a sanda suka haihu, inda suke dake ganyen ta su yi kunun gero suna sha dan kara yawan ruwan nono da kuma inganta lafiyar ciki.
-Ana amfani da garin ganyen sabara dan warkarda ciwon daji waton cancer a Turance.
-Ganyen sabara na maganin kumburin jiki da kaikayin jiki.
-Ganyen sabara na maganin kurajen kazzuwa da kurajen fiska masu kaikayi da kuma zafin jiki dama na ciki.
-Ganyen sabara na magance tarin asima da kuma tarin tibi.
-A kan gauraya garin ganyen sabara da garin bawon bagaruwa dan a yi maganin kuna a jiki.
-A kan hada wasu ganyayyakin itatuwa da ganyen sabara a tafasa ko a dake a maida su gari dan a iya warkar da basir, gudawa, cututtukan ciki, farfadiya, ciwon gabobin jiki, hawan jini, kuturta da dai sauransu.
-A kan yi amfani da danyen ganyen sabara dana nunu sai a tafasa macen dake jego sai ta rinka surace da ruwan hakan zai ba ta lafiya da karfin kassan jiki da kuma rage kumburin jiki ko na kafafuwa dama jin ciwo a bayan haifuwa.
-Macen dake shayarwa za ta iya fake shan kunun sabara dan ta tsabtace nononta dama kara yawan ruwan mamma.
-A kan tafasa saiwar sabara sai a tace ruwan a sha da safe kamin a ci abinci dan kashe tsutsar ciki.
-Ana tafasa saiwar sabara da kuma kirya sai a rinka zama a cikin ruwan dan magance basir maisa kaikayin dubura da kuraje ga dubura kai har da basir mai tsiro.
-Ana amfani da sabara dan magance kurajen da suka yi lailayi a cikin baki ko harshe.
– Ana shan cokali daya karami misalin 5ml na garin sabara a cikin nono sai a sha a sanda ake fama da dan kanoma.
-A nasu tsarin maganin gargajiyan, Sudan su kan yi amfani da ganyen sabara su yi maganin ciwon suga.
-Sabara na maganin amosanin kai da kuma iskan dake ma yawo a cikin jiki kamar tana.
-Ana tauna danyen ganyen sabara a hadiye ruwan dan magance kuraje a cikin wuya ko ciwon makogwaro da jin zafin hadiyar yawu.
Gargadi
– Magani ba abinci bane don haka a kula ba kowane ciwo ake shawa Sabara ba, kuma ba komai za ka ga ko za ka ji bayaninsa sai kaje ka nema da kanka ka hada ka sha ba, babu wani maganin da ake yiwa izgilanci kamar na gargajiya, kada ka zamo likitan kanka, ilimi ne idan ba ka da shi to ka tambayi masana. Masu iya Magana na cewa “mataibayi ba ya bata”. Allah ya ba mu ikon kiyayewa, amin summa amin.
© Sirrinrikemiji
Post a Comment