Shugaban jam'iyyar adawar Danmak ya kone littafin Al Kur'ani mai Tsarki kurmus,da nufin nuna kin amincewarsa da jajantawar da Musulman kasar ke yi wa 'yan uwansu na New Zealand.

Dan siyasar ya aikata wannan ta'asar a daidai lokacin da Musulmai ke gudanar da sallar Jumma'a a gaban majalisar dokokin kasar,duk da cewa shugabannin Danmak ne suka bai wa mabiya addinin Islama izinin yin hakan da nufin ba su damar nuna bacin ransu dangane da kazaman hare-haren ta'addanci da aka kai wa 'yan uwansu na New Zealand a makon da ya gabata.

An sanar da cewa, bayan aika-aikan na dan siyasa Rasmus Paludan shugaban jam'iyyar Stram Kurs,akwai wasu gungun masu tsauraran ra'ayoyi,wadanda suka dinka daga tutar Isra'ila da kuma busa kahonni don tayar da hanaklin Musulman.

TRThausa.

Post a Comment

 
Top