Hotunan bidiyo na batsa, hotuna ne masu motsi da suke da shafuka daban-daban a intanet a wannan zamanin. Kafin shaharar intanet a duniya, masu irin wannan ta’asa sukan yi amfani ne da kaset na bidiyo wurin yada badalar tasu, amma samuwar intanet sai suka samu ci gaban mai hakar rijiya. Galibi an fi ganin matasa su ke da kaso mafi yawa da ke kallon bidiyo na batsa, duk da cewa akwai sauran rukunin jama’a a matakai daban-daban da su ma za a iya samun su dumu-dumu suna kallo. Masu wannan halin anya kuwa kun san illolin haka?

– Shin kun san abubuwan da kuke kallo yana daga cikin manyan laifuka (kaba’ir ).

– Shin kun san abin da kuke kallo yana gadar da kaskanci da kuma rauni ta kowane bangare.

– Shin kun san abin da kuke kallo yana kawo raunin idanu da kwakwalwa da yawan mantuwa, abu kankani sai kamanta.

– Shin kun san wannan kallon yana sa mutuncin mutum ya fadi a idon Allah.

– Shin kun san wannan kallon yana hana mutum samun ilimi ko mantashi.

– Shin kun san wannan kallon yana hana ka /ki samun jin dadin rayuwar aure mai inganci da mijinki ko matarka, kuma duk da kuna son juna.

– Shin kun san cewa za ku iya mutuwa a cikin wannan yanayin (mummunar cikawa).

– Shin kun san jikinku zai gaya muku ko badade ko bajima in baku tuba ba.

-Shin kun san duk abin da kuka yada kuna da zunubi, imma ya yi sanadiyyar lalacewar wani kuna da zunubin ko da kuna kwance a kabari har izuwa kiyama.

– Shin kun san cewa duk wanda yabar wani abu domin Allah, Allah zai musanya masa da abin da ya fishi alkairi.

– Shin kun san cewa Allah yana farin ciki sosai da tuban bawansa.

– Shin kun san cewa Allah zai wadata ku da falalarsa idan kuka kame kawunanku daga aikata haramun.

– Shin kun san cewa sha’awar ‘yan mintina ta haramun tana dai-dai da azabar shekaru.

‘Yan uwa musulmai ku taimaki ‘yan uwammu wajen isar musu da sakon nan ko allah zai shirya su ta dalilin ku sai ku samu lada.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top