Harkar tsaro aba ce da ta shafi kowa da kowa. A kwai wadansu matakan tsaron da ya kamata mu dinga dauka a gidajenmu, domin tsaron rayuwarmu da kuma na iyalanmu baki daya. Matakan su ne:

1. Kada ka bari ‘ya’yanka wadanda basa iya gane muryar mutum su bude wa bako kofa.
2. A yi kokari a gane muryar baki kafin a bude musu kofa.
3. Kulle dukkan kofofin gidanka lokacin da kake cikin gida, musamman da yamma.
4. Ka kashe duk na’urorin lantarkinka, kafin ka fita, koda a lokacin fitarka babu wutar lantarki.
5. Binciki kayan da kuke dafa abinci, kafin ka fita.
6. Ka guje wa namijin da ya yi kama da mace mai ciki, watakila yana dauke da wani bin da zai cutar da mutum ne.
7. Ka kulle motocinka koda kuwa ka shigo da su cikin gida.
8. Kare makullan abin hawanka daga yiwuwar sacewa da yin kwafin makullin.
9. Kare katin layin wayarka (sim card) da barayi don za su iya amfani da shi wajen yin cinikin kudin fansa.
10.Sayi abubuwan kashe wuta a motarka da kuma gidajenka.
11. Ka gaya wa malaman ‘ya’yanka kada su ba da su ga kowa, sai da izinka.
12.Kada ka bari bakon da ba ka sani ba ya kwana a gidanka, ka tura shi zuwa ga ofishin jami’an tsaro.
13. Kada ka aika da nambar katin cire kudi (ATM), ko kuma nambar BBN dinka ga kowa.
14.Kada ka biya kudin sayan kowace irin mota ta kafar intanet, idan baka tabbatar da mai sayar da motar ba.
15.Kada ka bari yara kanana su je makaranta su kadai.
16.Kada ka yi tafiya ba tare da ka sanar da wani ba.
17.Ba da rahoton duk wadanda kake zargi da laifi wajen ‘yan sanda ko dakarun soji ko kuma hukumar tsaron farin kaya da sauransu.
Da fatan za mu aiki da wadannan matakai domin kare lafiyar kanmu da ta iyalanmu.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top