Tsohon Gwamnan Kano,Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya wallafa rubutu a shafinsa na facebook cewa ba a yin zabe a jihar Kano gaba daya sai murdiya kawai ake yi yanzu haka.

Sannan ya yi sharing link yake cewa Mataimakin babban Sufeta Janar na 'yan sandan Nijeriya DIG Anthony Ogbizi Michael da aka turo Kano ya zo ya karbi ragamar umarni da tabbatar da tsaro ya wargaza dukkan tsarin da aka yi na tabbatar da tsaro.

A gefe daya kuma, Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Kano Rabiu Sulaiman Bichi ya bayyana ya nemi a soke zaben da ake kan gudanarwa a Kano saboda rashi tsaftarsa

Bichi ya bayyana bukatar hakan ne yayin zantawa da manema labarai a yau din nan, inda yace abinda ke gudana ba zabe ba ne illa
shiririta.
Rariya.

Post a Comment

 
Top