Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fada wa mambobin jam’iyyar sa, APC, cewar ba zai saka baki a zabukan da za a maimaita a wasu jihohin kasar nan ba.

A wani jawabi da kakakin sa, Malam Garba Shehu, ya fitar a yau, Lahadi, Buhari ya bayyana cewar ba zai yi Magana da hukumar zabe ta kasa (INEC) ba domin ta yi alfarma ga ‘yan takarar jam’iyyar APC ba.

A cikin jawabin, shugaba Buhari ya gargadi ‘yan siyasa a jihohin da za a maimaita zabukan da su guji amfani da kalaman da kan iya tunzura ma su zabe gabanin zabukan da za a maimiata.

Kazalika, jawabin ya yi tir da kalaman wadan su, musamman ‘ya’yan jam’iyyar APC, da ke sukar shugaba Buhari a kan ya ki saka baki domin ‘yan takarar jjam’iyyar APC su sami alfarma.
Buhari
Shehu ya kara da cewa: “tsofin shugabannin Najeriya na baya na saka baki a duk lokacin da za a maimaita zabe, kuma hakan ne ya sa wasu ke ganin laifin shugaba Buhari yanzu saboda bai saka baki ba tare da sun yi la’akari da cewar shugaba Buhari daban yake ba. Ya yi rantsuwa a kan kare martabar kundin tsarin mulkin Najeriya kuma ba zai yi duk wani abu da ya saba wa haka ba .

Yace “Kundin tsarin mulkin Najeriya bai bawa shugaban kasa ikon yin haka ba. Abun dariya ne da ban mamaki a soki shugaba Buhari a kan bai yiwa kundin tsarin mulki karan tsaye ba.

“Wani abun mamaki ma shine yadda ‘yan jam’iyyar adawa ke suka da zargin shugaba Buhari a kan yana son yin amfani da karfin gwamnatin tarayya domin bawa ‘yan takarar jam’iyyar APC sukunin lashe zabe.”
“Ya kamata ‘yan APC a jihohin da za a maimaita zabe su sani cewar alhakin jam’iyya ne ta yi aiki tukuru domin tabbatar da samun nasara ba wai zaman jiran tsammanin shugaba Buhari ya umarci INEC ta murde zabe ko yin alfarma ga ‘yan takarar APC ba .”


©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top