Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce zai dauki dangana idan ya sha kaye a zaben gwamnan jihar wanda za a kammala a ranar Asabar.

Gwamna ya bayyana hakan ne lokacin wata hirar musamman da ya yi da BBC a Kano ranar Alhamis.

"Idan wani ya ci zabe ba ni ba, Allah Ya kiyaye, zan taya shi murna kuma zan karbi sakamakon da hannu biyu-biyu," in ji Gwamna Ganduje.

A bangare guda kuma ya ba magoya bayansa tabbacin cewa ba shi da wata fargaba saboda "da yardar Allah za mu ci wannan zabe."

Siyasar Kano tana ci gaba jan hankali, saboda girman hamayyar da ke tsakanin manyan jam'iyyun siyasa guda biyu APC da PDP .

Fafatawar a zaben da za a sake a Kano ta shafi 'yan takarar manyan jam'iyyu biyu ne gwamna Ganduje na APC da kuma babban mai hamayya da shi Abba Kabir Yusuf na PDP.

Sai dai gwamnan ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda Kwamishinan 'Yan Sandan jihar CP Mohammed Wakili yake tafiyar da aikinsa a jihar.

"Alakar aiki ce ke tsakanina da CP Wakili, amma kuma kamun ludayinsa akwai ayar tambaya gaskiya. Mutane da yawa suna ganin ya dauki bangare a wannan harka ta siyasa," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: "Magana ta biyu ina ganin aikinsa yana yi masa rikon sakainar kashi."
BBChausa.

Post a Comment

 
Top