AURE

Da farko yake yar’uwa ki sani aure bautanena ubangiji ne. To amma mai yasa ku mata kuke banbanta yanayin zaman aurenku bayan Annabinmu dayane, domin da yawa daga cikin yan uwa mata basu dauki aure a matsayin bautaba wallahi.

Bayan aure itace babban hanyar shigarki Al-jannah idan kikayi hakan kuma kika yarda da hakan to kinci riban duniya da kuma lahira.Allah yasa haka Ameen. Sannan ki sani yar’uwa duk wata ibada tana tareda jarrabawa musamman ma aure, domin zamane da ya kunshi farin ciki da bakin ciki, dadi. da mara dadi, hakuri da rashin hakuri, da sauran wasu abubuwan da basai na ambacesu ba, Yake yar’uwa ki sani aure anayinsa saboda wasu abubuwa da dama amma babban su shine natsuwa. Kuma natsuwa baya samuwa sai idan mace ta zama tagari shiyasa da yawa daga cikin maza basuda natsuwa saboda matansu ba nagari bane.

Manzon Allah (S.A.W) yace duniya abin jin dadi ne, amma mafi alkhairin jin dadin duniya shine mace tagari, don haka ya yar’uwata idan harke ba mace tagari bace to ki sani baki da amfani a zaman gidan aurenki da mijinki idan kika sake baki gyara zamanki da mijinki ba, to wallahi zaki samu mummunana sakamako a wurin Allah. Allah ya karemu Ameen.

 

FA'IDODIN YIN AURE

 

Duk wanda ya samu halin yin aure namiji ko mace, to za su wayi gari sun cimmawasu abubuwa da dama, ga kadan daga ciki:

(a:Sunyi biyayya ga umurnin Allah (SWA) kamar yadda ayoyi suka gabata.

(b:Sun bi sunnan Manzon Allah (SAW) sun yi koyi da shi, kuma za su samu natsuwada kwanciyar hankali.

(c:Sun yi maganin sha'awarsu ta 'yan Adam, sun kuma kare mutuncinsu.

(d:Sun biya bukatarsu ta hanyar da ta dace, ba ta tsinanniyar hanya ba!

(e:Sun taimaka wajen magance yaduwar barnace-barnace da ayyukan ash-sha

(f:Sun kara yawan al'ummar Manzon Allah (SAW), idan sun hayayyafa kamar yadda Annabi (SAW) yc"(Lallai idan kun yi aure kun hayayyafa) ZAN YI TAKAMA GA SAURAN AL'UMMA"[Abu Dawud 2050, Nasa'i 6/75]

(g:Ga samun lada mai yawa a wurin Allah, domin ladan aure kamar na sadaka ne,don Annabi (SAW) yc "A CIKIN JIMA'IN DAYANKU MA AKWAI (ladan) SADAQA

SIFFOFIN WANDA AKE SO A AURA. 

Akwai siffofi da ake so, miji da mata su kasance sun siffantu da su, tun kafin sunemi junansu da aure, don samar da farin ciki da natsuwa a tsakaninsu, ga su nankamar haka:-

(1) SIFFOFIN NAMIJIN DA ZA A AURA:-a.Ya zama mai addini, mai kiyaye dokokin Allah, ko da kuwa ba malami ba ne, donmai addini shi ne ake tsammanin kiyaye hakkokin auratayya daga gare shi.

(b.Ya kasance ya dan haddace wadansu Ayoyin Alqur'ani, don sukan kara wa bawaImani, wanda ya haddace ayoyin kuma yana kiyaye dokokinsu babban mutum ne awurin Allah.

(c.Ya zama mai tausayin mata, ba mai duka, zagi, takuri da cin mutunci ba, a indababu gaira babu dalili.

(d.Ya kasance yana da kuzarin biyan bukatan Iyalinsa da nemo mata abinci, suturi,wurin zama da abubuwan masarufi na yau da kullum tun da Annabi (SAW) yc"WANDA YAKE DA HALI DAGA CIKINKU YA YI AURE..." [Bukhaqi 5065, Muslim1400].

(e.Wanda ganinsa zai faranta ran matarsa, da samun zamantakewa mai kyau.

(f.Ya kasance ana tsammanin samun zuriya daga gare shi, akan gane hakanne tahanyar 'yan uwansa ko zuriyars. Ko da yake haihuwa ta Allah ce, yana bayar da itaga wanda ya so, kuma yadda ya so, wani kuma sai ya sanya shi AQIM, kamar yaddayc"YA KAN SANYA WANDA YA GA DAMA AQIM (wanda ba ya haihuwa)" [Shura50].

(g.Kuma ya kasance ya dace da matar, ta wajen hali, matsayi da fahimtan juna, donsamun zaman lafiya. Anan nake jan hankalin 'yan uwa mata da kada su kuskura suauri mutumin banza, mai halin mutanen iska, don za su shiga mayuwacin halin da zaisa ba za su ji dadin rayuwarta ba har abada! Duba (Sahih Fiqhis Sunnah 3/103-107).

 

SIFFOFIN MACEN DA ZA A AURA

(a.Takasance ma'abuciyar addini. Annabi (SAW) yc"...KA RABAUTA DA MAI ADDINI, ZA KA YI RIBA" [Bukhari 5090, Muslim 1466]

(b.Ta kasance tana da kyau, hali da mutunci, kamar yadda Annabi (SAW) ya faralissafawa a Hadisin da muka ambata a sama.

(c.Ta zama mai tausayi da kauna, wanda ba za ta azabtar da miji ko wulakanta shiba, don Annabi (SAW) yc"WADANNAN SU NE MAFIYA ALHERIN MATA".

(d.Ta kasance tana da amana da biyayya, Annabi (SAW) ya yaba wa irin wadannanmatan, amma mace fitsararriya ko shedaniya babu abinda za a samu daga gare tasai fitina da tashin hankali.

(e.Ta kasance budurwa, wanda wani bai taba saninta ba, don akwai wanda ya yiaure a zamanin Annabi (SAW) sai ya tambaye shi, "BUDURWA CE KOBAZAWARA?" sai ango ya amsa da cewa: Ai bazawara ce! Sai Annabi (SAW) yc "AI DA BUDURWA CE (ka aura), KA YI WASA DA ITA, (itama)TA YI WASA DA KAI!"(Bukhari 5079, Muslim 715). Ba wai an hana auren Bazawara bane, matukar ansamu fahimta, sai dai ba a san abin da ya koro ta daga gidan mijin farko ba, donhaka a yi kokarin kiyaye martabar aure, idan anyi sakin nan ba alheri ba ne, idanbabu dalili.

(f.Ta kasance mai haihuwa, saboda Hadisin da ya gabata a can baya na yawaitaral'ummar Annabi (SAW) da yin aure, ga wanda Allah (SWA) ya kaddara mu suhaihuwa.Wadannan siffofi su ake bukata ga ma'aurata su siffantu da su, don tabbatar daalherin aure da samar da natsuwa da kwanciyar hankali duniya da lahira. Allah yaazurta mu da mata na gari haka su ma matan ya ba su mazaje na gari.

 

YADDA AKE NEMAN AURE DA KULLA SHI

Idan NAMIJI ya ji yana kaunar wata mace, kuma yana son ta da aure, to ya halattaya kalle ta yadda ya dace, don tabbatar da abin da ya yi niyya, idan Allah (SAW) yayarda.Wannan gani da zai yi mata, musulunci ya halatta masa, tun da gani ne na nemantabbatar da alheri bana barna ba, bayan samun izinin waliyyanta, bayan ya ganta,sun zanta sun amince da juna, to haramun ne kuma wani ya yi kundumbala ya shigo,saboda fadin Annabi (SAW):"KA DA WANI YA YI NEMAN AURE AKAN NEMAN DAN UWANSA, HAR SAI YABARI (idan ba a samu amincewa ba), KO KUMA SAI MAI NEMAN YA BA SHI IZINI(Idan ya ga kamar ba zai kai labari ba)" [Nasa'i 6/73 don karin bayani duba littafin ALWAJIZ 281-282]. Amma idan manemin mutumin banza ne, malamai sun yi bayanin cewa ya halattaa wargaza shirinsa.Idan namiji zai yi zance da mace, to a kiyaye wadannan sharudda:

(1.Kada ya kebanta da ita a wani wuri na daban, ya zama na suna tare damuharransa mata, ko kuma nata maza don kar su yi barna.

(2.Kada ya yi mata kallon jin dadi ka na sha'awa.

(3.Kada yayi hannu da ita, ko ya taba jikinta, don bata halatta masa ba, har sai andaura aure.

(4.Ya zama da kyakkyawar niyyar zai aure ta ne.

(5.Ya halatta ya yi zance da ita, ya tambaye ta, ta tambaye shi, abinda ya dace,don su fahimci juna, don kar a yi aure, daga baya a zo ana dan da na sani.

(6Kada ya fita da ita yawo, ko shakatawa, ko da an yi masa alkawari, yinharamunne, ko da kuwa babu abinda zai faru, fita da ita bai halatta masa ba, har saian yi aure (Baiko fa ba aure ba ne tun da ana iya warware alkawarin saboda wanidalili, don haka sai a yi a hankali).duba (FIQHUS SUNNAH LINNISA'I na Abu Malik da BAIKO BA AURE BA NE naMal. Ahmad Murtala Kano).Da za a kiyaye wadannan sharrudan, da za a samu natsuwa da jin dadi, rashinkiyaye su ne ya haifar mana da abubuwan takaici da 'ya'yan shegu marasa asali.

 

Idan abubuwa sun daidaita, sai batun daura aure tare da kiyaye wadannansharrudan:

 

(a.Waliyyi:- Doe ne a samu yardarm waliyyi, don duk auren da aka daura ba tare dayardar waliyyi ba, to auren bai yi ba, idan akwai rikici ko matsala, sai shuguba yashiga maganar ya warware ta, amma ta hanyar da ta dace.

 

Don duk matar da ta daura aure wa kanta, ba tare da waliyyinta ba, ta zama karuwadomin:

"MAZINACIYA ITA CE TAKE AURAR DA KANTA". Anan nake jan hankalin iyaye su daina yiwa 'ya'yansu auren dole, don hakan badaidai ba ne, kuma hakan yana haifar da illoli masu yawan gaske, Annabi (SAW)yake cewa "A NEMI SHAWARINSU, A TAMBAYE SU, DON A SAMU DAIDAITO".Don haka iyaye sai a hankata, a bar yarinya ta auri wanda take so.(b.Sadaki:- Dole ne a bayar sadaki a bisa abin da aka amince a kansa, mai sauki,wanda babu tsanani a ciki, don samun karin albarka a wurin Allah (SWA). Annanbi(SAW) yace:- "ALBARKAN AURE YANA DAGA KLARANCIN SADAKLI". Allah (SWA) yana cewa "KU BA WA MATA SADAKINSU, KYAUTA CE (daga Allah,da dadin rai)" [Nisa'i 04].Don haka sadakin na mata ne, kuma idan babu matsi sai a bayar da yawa babulaifi, don sadakin Annabi (SAW) yana da yawa. Amma batun dole kayan aure sai yakai kaza ko sai anyi akwati adadi kaza, wannan baya cikin sharadin aure, da fataniyaye da 'yan mata za su hankalta (An kusa a fara kai kayan aure a gari ya yi zafi koakwati mai Giwa).(c.Kulla aure: wasu kalmomi ne da ake amfani das u na nema da bayarwa, idan anyi wannan tsakanin waliyyin mace da miji ko wakilinsa, shi ke nan, aure ya kullu, saia sanar da jama'a. Amma zuwa wuraren barna na masha'a tare da maza da mata, haramun ne, bamusulunci ba ne yahudanci ne, kuma irin wannan baya albarka, kuma da wuri yakelalacewa, Allah ya sauwake.Bayan an gama wannan, sai mata ma su hankali da natsuwa su dauki amarya sukai ta gidan mijinta, tare da yin nasihohi ko bayar da shawarwarin da suka dace, dontabbatar da zaman lafiya da samun arziki.Don karin bayani a duba [FIQHUS SUNNAH na Sayyid Sabiq, da ADABUZ ZIFAFna Albani].

 

FADAKARWA

(a.Idan an daura aure, kafin matar ta tare a gidan mijinta, ko bayan ta tare, ana sona gabatar da walima. Walima sunnah ce mai karfi, a yi ta da abin da Allah (SAW) yahore, ko da taimakon da za a samu, a tara mutane maza ne ko mata bisa tsarinShari'a, a ci abinci, wannan shine walima. Mata na iya shirya walimarsu matukarbabu sabon Allah a ciki,duba littafin [AZZAWAJ na Dr. Muhd Ibrahim Alhafnawy 41]. Annabi (SAW) ya yi walima, kuma ya kwadaitar da Sahabbansa (RA), da su yi ta,har ma yace wa Anas bin Malik (RA) yayin da ya yi aure: "KA YI WALIMA KO DA(yankan) DAN AKUYA NE" [Bukhari 5169].Kuma duk wanda aka kira shi dole ne ya amsa, sai dai idan yana da uzuri, sai yasanar, kuma duk wanda ba kira shi ba, idan ya je, ya yi laifi.(b.Taya ma'aurata murna da farin ciki sunna ce, tare da yi mu su addu'a, kamaryadda Annabi (SAW) yake yi 

Kuma haramun ne bayyana asiran saduwa da iyali,

 

 Annabi (SAW) yace "DUKWANDA YA YI HAKA SHI NE MAFI ASHARARAN MUTANE RANAR ALQIYANAH"[Muslim 1437, Abu Dawud 4870].Da za a kiyaye wadannan da za a samu albarkar aure, 'ya'ya da zuriyya, Insha Allahu.HAKKOKIN MACE AKAN MIJINTA.Wadannan hakkokin, kiyaye su shi ne kashin bayan tabbatuwar aure da ni'imarsa,rashin kiyaye su kuwa babbar matsala ce, ga su nan kamar haka:

 

(1.Samar mata da wurin zaman da ya dace don kare mata mutuncinta, kamaryadda Allah (SWA) yc"KU ZAUNAR DA SU A INDA KUKE ZAUNE GWARGWADON SAMUNKU" [Dalaq6].

 

(2.Dole ne ya sama mata abinci gwargwadon karfinsa, kamar yadda Allah (SWA) yc"MAI WADATA YA CIYAR DAGA WADATARSA, WANDA KUMA AKA KUNTATAMASA ARZIKINSA, TO YA CIYAR DAGA ABIN DA ALLAH YA BA SHI" [Dalaq 7].

 

(3.Ya tufatar da ita a lokacin da ya dace, gwargwadon halinsa, Annabi (SAW) yc"KA TUFATAR DA ITA, IDAN KA TUFATAR DA KANKA" [Abu Dawud 2142, IbnuMajah 1850].

 

(4.Biya mata bukatarta ta 'ya mace wannan dole ne, gwargwadon yadda llAllah(SWA) ya halicce su, haka zai taimaka wajen tsare mata mutuncinta, kuma hakki nebabba, kamar yadda Annabi (SAW) yake cewa"LALLAI GA IYALINKA AKWAI HAKKINTA A KANTA" [Bukhari 1977, Muslim1159].Duk wanda yake tare da iyalinsa, har ya kaurace mata tsawon watanni 4 babusaduwa, sai ta yi karansa wajen magabata, ko ya sake ta, ko ya dawo ya gyara hali,wannan ai cutarwa ce babba.(Wannan shi ake kira IYLA'I, kamar yadda ayoyin Bakara suka yi bayani, dubabayanin Malamai a cikin ALFIQHU ALAL MAZAHIBIL ARBA'AH na Abdurrahman Aljuzairy).

 

(5.Dole ya karantar da ita yadda za ta bauta wa Allah (SWA), ko dai ya yi da kansako ya roki wani, ko ya dauki nauyin hakan.Rashin koyar da mata addini hatsari ne babba, don kusan duk tarbiyar gidan ahannunsu take, idan ba su san addini ba, yaransu za su tashi sun fi su lalacewa, saidai wani ikon Allah.Koyar da ita addini shine kare kai da iyalai daga shiga wuta, kamar yadda Allah yayi umurni a inda yake cewa"YA KU WADANDA SUKA YI IMANI, KU TSARE KANKU DA IYALANKU DAGAWUTAR DA MAKAMASHINTA MUTANE NE DA KUMA DUWATSU.." [Tahrim

 

6]. Amma koyar da ita wani ilimi ko sana'a wannan cigaba ne da samun saukintaimako a rayuwa.(6.Ka da ya cutar da ita, da duka, zagi, musgunawa da kaskantarwa, don macetana da daraja a wajen Allah (SWA), duk abin da ya faru sai a bi dokokin da Allah yagindaya, kar a bi son zuciya. Hakuri da danne zuciya suna da muhimmanci a cikin

al'amuran duniya, ba ma a na aure kawai ba, don haka abin da bai taka kara ba balleya karya, bai kamata ya zama bala'i ba.Idan mace ta yi laifi har ga Allah, akwai mataki guda 3 kamar haka:

 A .WA'AZI: Za a yi mata wa'azi na bayanin muhimmancin biyayya da illar saba wamiji ko bala'in saki (Idan Allah ya ba mu lokaci za mu tattauna akan SAKI insha Allahu).

 

B .KAURACEWA: Idan wa'azi bai yi ba sai a kaurace mata a wajen kwanciya, a kikulawa da ita a cikin dakinta, amma dole ne a bata abinci don Annabi (SAW) yc"KADA KA KAURACE MATA SAI A CIKIN DAKI" [Abu Dawud 2142, Ibnu Majah1850 da Ahmad 4/447].

 

C .DUKA: Daga nan kuma sai dukan ladabtarwa, ba mai cutarwa ba, ban da dukanfiska, ban da zagi ko bakaken maganganu, ba kuma a gaban yara ko a waje ba. Idanabu ya faskara kuma sai a je wajen magabata don su warware matsalar. Wadannanmatakai guda 3 Alqur'ani ne ya ambace su. Duba [Suratul Nisa'i 34].Wannan shine tsari, daga nan kuma, ko a yi sulhu ko a rabu, Allah ya sauwake.

 

(7.Rashin bayyana sirrinta: Haramun ne ya bayyana sirrinta, kamar yadda ita maaka haramta mata bayyana nasa. Annabi (SAW) ya yi gargadi akan bayyana sirrin juna, tun da an hadu dama dole ne kowa yasan asirin kowa.

 

(8.Lallai ne a ba ta izinin fita idan ya zama dole ko ya kama, don zuwa Asibiti,Makaranta, gidan Iyaye ko na 'yan uwa, da sharadin rashin aukuwar fitina, idanakwai matsala sai a dauki matakin gyara.

 

(9.Dole ne ya yi wa matarsa kyakkyawan zato, ban da tuhuma, zargi da dari-dari,idan har akwai shakku to sai ya dauki matakin gyara a zahirance ba a munafunce ba. 

 

Allah (SWA) yc"YA KU WADANDA KUKA YI IMANI, KU NISANCI DA YAWA DAGA ZATO,LALLAI WANI SASHIN ZATO LAIFI NE, KA DA KU YI LEKEN ASIRI..." [Hujrat 12].Shi ya sa ma Annabi (SAW) yc"IDAN MUTUM YA YI TAFIYA KADA YA DAWO GIDA DA DADDARE KWATSAM,BA TARE DA YA SANAR DA IYALANSA BA" [Bukhari 5244].Kuma idan mijin mace ba ya nan, idan ya kama a shiga wurinta, to duk wanda zaishiga ka da ya je shi kadai, ya neni wani muharraminta, ko wasu mata, don kauce wamummunan zargi.

 

(10.Yin adalci dole ne ga matan da suke da yawa wajen mazauni, tufafi, abinci daabubuwan masarufi. Amma a bangaren sadaki, walima da kauna, ba lallai ne ya zama daidaiwa daida ba, ana iya samun bambanci, Allah (SWA) yc"BA ZA KU IYA YIN ADALCIN (So da Kauna) A TSAKANIN MATAYENKU BA, TO AMMAKA DA KU KUSKURA KU KARKATA (Zuwa ga Mowa) GABA-DAYAN KARKATA, KUKYALE (Wancar Boran) KAMAR WADDA AKA RATAYA (ba a kallonta sai za a yi amfani daita)" [Nisa'i 129].Kauna da So suna samun asali ne saboda; hankalin mace, kyawunta, kudinta, komatsayin iyayenta, ds, don haka ayi dai a bi hankali ya ku mazaje kar a fada cikin halaka!Don haka adalci dole ne a tsakanin mata da 'ya'ya, idan mutum ba zai iya yin adalcin ba,sai ya tsaya ga mace daya, kamar yadda Aya ta nuna, [Nisa'i 03].Mace dayan ma dole ne a kiyaye mata hakkokinta, idan ba haka ba asha azaba.

 

(11.Yin ado da kwalliya wa mace hakki ne, don ka da hankalinta ya karkata zuwa gamazajen waje. Ibnu Abbas (RA) yc "LALLAI NI INA SON IN YI ADO WA MATATA, KAMAR YADDANAKE SON TA YI MINI, SABODA ALLAH (SWA) YANA CEWA: "SU MATAN SUNA DA IRIN ABIN DA YAKE KANSU (na hakkoki a gare ku)

 DA KYAUTATAWA" [Bakara 228].

 

(12.Yin wasanni, sake fuska, tattaunawa da hira hakki ne mai tabbatar da zaman lafiya atsakanin ma'aurata, kamar yadda aka samo cewa Annabi (SAW) yana wasa da matansa,yana hira da su, yana sake musu fuska. Yace"MAFI ALKHAIRINKU SHI NE MAFI ALKHARI WA IYALANSA, NI KUMA (Annabi SAW)NA FI KU ALKHAIRI WA IYALINA" [Tirmizy 3892, Ibnu Hibban 1312].

 

(13.Dole ne a yi mu'amala mai kyau ga iyalai, hakan shi zai tabbatar da dorewar ci gaba,kwanciyar hankali da more rayuwar duniya da lahira. Idan suna da yawa zai taimaka wajensassauta mumnunan kishi da kiyayya a tsakaninsu da rigingimun da babu gaira babu dalili.Kiyaye wadannan hakkoki na mata shine zamantakewa mai kyau da samun arziki daalbarka, Allah (SWA) yc"KU ZAUNA DA SU DA KYAUTATAWA (mai kyau)" [Nisa'i 13].HAKKOKIN MIJI AKAN MATASA

 

(1.Dole ne ta yi masa biyayya, ga abinda yake ba sabo ba ne, Annabi (SAW) yc "BABUBIYAYYA A CIKIN SABON ALLAH, ABIN SANI DA'A TANA CIKIN ABIN DA SHARI'A TASANI NE" [Bukgari 7257, Muslim1840].

 

(2.Ta zauna a gida ban da yawace-yawace, ban da fita sai da yardarsa.

 

(3.Ta amsa masa idan ya nema ta, ba tare da matsala ba.

 

(4.Ka da ta bar wata ko wani ya shiga gidansa sai da yardansa, Annabi (SAW) yc "KADAWATA MATA TA BAYAR DA IZININ (shiga) GIDAN MIJINTA, ALHALI YANA NAN, SAI DAYARDARSA" [Muslim 1026] amma idan bai yarda ba, ko baya nan bai halatta ta bar wata kowani ya shigo gidan ba.

 

(5.Ba za ta yi azumin nafila ba, idan yana nan, sai ya yarda, saboda Hadisin da ya hanahaka.

 

(6.Ba za ta dauki wani abu daga dukiyan mijinta ta bayar ba, sai ya amince, Annabi (SAW)yc "KA DA MACE TA BAYAR DA WANI ABU DAGA GIDAN MIJINTA SAI YA YARDA" [AbuDawud d.s].

 

(7.Za ta yi hidima wa mijinta, da kula da al'amuran yaransa, kamar abinci, wanki, share-share d.s, daidai gwargwado, tun da zaman aure zama ne na cude ni in cude ka.Nana Fatimah (RA) diyar Annabi (SAW) tana aikin wahala ainun a gidan mijinta Aliyu bin Abi Dalib (RA) [Bukhari 5361, Muslim 2182].Nana Asma'u (RA) diyar Abubakar (RA), ita ma tana hidima ainun, har kulawa sosai take yida dokin mijinta [Bukhari 5224, Muslim 2182].Idan miji ya samu dama sai ya sauwake wa matansa, ko ya rinka taya su, don Annabi(SAW) ya kasance yana taya matansa aikace-aikacen gida, idan an yi kiran sallah sai ya fita,ya tafi masallaci, kamar yadda Hadisin Nana Aishatu (RA) ya nuna. [Bukhari 676

 

(8.Wajibi ne ta kare mutuncinta, na mijinta da na 'ya'yansa da kuma dukiyarsa, bandaalmubazaranci, Allah (SAW) yc"MATAYEN KWARAI, MA SU KARKANTAR DA KAI NE, MA SU KIYAYE (mutunci dadukiya ne) GA GAIBIN DA ALLAH YA KIYAYE" [Nisa'i 34] <Ya Allah ka ba mu mataye nakwaira>.

 

(9.Ta gode masa idan ya yi abin kirki, ka da ta muzunta masa, ko ta yi masa gori, kumaduk abin da ya samo ya kawo gwargwodon halinsa, ta karba hanu bibbiyu, don Annabi(SAW) yc"ALLAH BA YA KALLON RAHAMA WA MATAR DA BA TA GODE WA MIJINTA, KUMABA TA WADATUWA DAGA GARE SHI (da duk abin da ya yi) [Nasa'i 249]<Ya Allah ka tsaremu da irin wannan matan>.

 

(10.Yin ado wa miji da gyara jiki shi ma babban hakki ne, Annabi (SAW) cewa ya yi:"FIYAYYEN MACE, ITA CE WADDA ZA TA FARANTA MA KA IDAN KA DUBE TA"[Nasa'i da Ahmad].

 

(11.Ka da ta cutar da shi ko ta bakanta masa rai, saboda idan ta yi haka, matansa na Aljanna wadanda suke jiransa za su tsine mata, su la'ance ta, su ce: "...YA SHIGOWAJENKI NE FA KAWAI! KWANAN NAN ZAI RABU DA KE YA DAWO WURINMU" [Tirmizy1184, Ibnu Majah 2014].<To fa mata! Kun ji matanmu na Aljannah abinda za su ce!>

 

(12.Ta yi wa iyayensa da 'yan uwansa mu'amala mai kyau, don haka zai sa ta samukarbuwa a wurinsu, su rinka yi mata addu'a ta fatar alheri.Mu'amala mai kyau, ita ce: Sake musu fiska, maraba da su, ba su abinci, kyautata musuds.

 

(13.Ka da ta kuskura ta nemi SAKI, sai idan abu ya gagara, kuma ta hanyar da ta dace, Annabi (SAW) yc"DUK MATAR DA TA TAMBAYI MIJINTA SAKI BA TARE DA WANI LAIFI BA, TOHARAMUNNE TA JI KANSHIN ALJANNA" [Tirmizy 1199, Abu Dawud 2209 ds].Wadannan sune hakkokin da aka dora wa mace dangane da mijinta, idan ta kiyaye su, zata zama ta kwarai, kuma daya daga cikin manyan matan Aljannah, kamar yadda Annabi(SAW) ya bayyana da cewa:"IDAN MACE TA SALLACI (salloli) BIYAR DINTA (na farilla), TA YI AZUMIN WATAN TA(na Ramadan), TA KIYAYE FARJINTA (daga lalata), TA YI BIYAYYA GA MIJINTA, SAI ACE MATA "KI SHIGA ALJANNA TA KOFOFIN DA KIKA GA DAMA"" [Ibnu Hibban 4163].

Wannan Mata itace mace saliha, mai samar da annashuwa da albarkan duniya da lahira,don Annabi (SAW) yc"DUNIYA JIN DADI NE DAN KADAN, AMMA FIYAYYEN JIN DADINTA ITA CE MACESALIHA". Allah ya ba ku ikon kiyayewa amen.Da ma'aurata za su kiyaye wadannan hakkoki da tsakaninsu, wallahi da an samu zamanlafiya da natsuwa a duniyar aure gaba daya, kuma da lahirar ma tayi kyau. ALHAMDU LILLAH!KAMMALAWAWannan shine karkashen dan abin da Allah (SWA) ya ba ni ikon rubutawa dangane da abinda ya shafi sha'anin Aure. Allah ya gafarta mun ni da ku gaba daya. Da fatan za ku sanya ni a du'a'inku na alkhairi.

ABUNDA ANGO YAKAMATA YAYI YAYIN SADUWAR FARKO

 

An fi son miji yaje ma matarsa da hira kuma kada yayi gaggawar nuna mata cewar yin jimai ya kawo shi kusa da ita, idan yana cikin hira da ita sai ya kwantar da kansa a kan kafafuwanta kuma yaci gaba da hirar sa.


In an dan dauki lokaci ana hira sai ya dauki daya daga cikin hannayensa ya dora a jikin ta kuma ya fara wasa da jikin nata a hankali, yana wansan yana cire mata kaya a hankali, yana wasa da cibiyarta kuma yana yin sama da hannun sa zuwa kirjinta a hankali, da zaran yakai hannusa a kan nononta, sai ya ci gaba da wasa da nonowan na ta a hankali, idan so samu ne sai yasa bakin sa akan nonowan kuma yaci gaba da wasa dasu a hankali


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top