Daga Datti assalafiy
Shugaba Buhari ya bada umarni wa shugaban hukumar Custom na Kasa Kanar Hamid Ali cewa a bude dukkan dakin ajiya na kayan abinci da sauran kayan masarufi (Ware Houses) na hukumar Kwastom da suke fadin Kasarmu Nigeria gabaki daya
Shugaba Buhari yace a bude dakunan ajiyar kayan, a rabawa dukkun marayun da suke fadin tarayyar Nigeria, yanzu haka an fara gabatar da tsarin, kuma an faro ne daga yankin Yarbawa har an kammala da yankin yarbawan, yanzu haka suna jihar Sokoto, za su bi kowace jiha a Nigeria
Yadda tsarin rabon kayan yake shine; kungiyoyi masu zaman kansu a Nigeria wanda suke da marayu a karkashin ikonsu, su zauna su rubuta adadin marayun da suke kula da su a kungiyance, da zaran anzo jihar da kungiyar take sai aje ofishin hukumar Kwastom a gabatar musu da list, zasu bada kayan bisa adadin marayun da aka tabbatar, kuma hukumar Kwastom zata biya kudin da za'a dauki kayan a kai zuwa gurin da za'a rabawa marayun
Amma jama'ar arewa ko kun san wani babban abin takaici? saboda tsabagen munafurci da makircin kafofin watsa labarai masu zaman kansu a Nigeria ba su yayata wannan babban abin alheri da ya fito daga gurin shugaban Kasa Muhammad Buhari ba, inda ace abin sharri ne to za'ayi ta yayatashi
Ni kaina ban san da wannan tsarin ba sai ranar da nayi Posting akan wata kungiyar iyaye mata Musulmai da suke taimakon marayu, sai wani mutumina babban jami'i a hukumar Kwastom ya karanta rubutun da nayi ya kirani a waya yake sanar dani, har ya tabbatar min da cewa rabon kayan da akayi a Lagos yana ciki
Sannan wani karin abin takaici a rabon kayayyakin da aka faro daga yankin Yarbawa duk kungiyoyin da suke zuwa da list na marayu mafi yawancinsu kungiyoyin mabiya addinin Kirista ne, mu musulmai an barmu a baya, amma wannan matsalar ta faru ne a dalilin rashin yayata labarin da akayi
Ina kira ga kungiyoyi masu zaman kansu da suke tallafawa marayu wadanda suke wannan yanki namu na arewa su farga da wannan babban abin alheri da ya fito daga gurin shugaba Bujari, ina bada shawara ga jagororin kungiyoyin suyi gaggawa zuwa ofishin hukumar Kwastom dake kusa da su suyi tambaya akan wannan abin alheri, sannan a tambayi ranar da za'azo ayi rabon kayan a jihar da ake, sai ayi tanadi
A taimaka a yada wannan sanarwan don Allah
Shugaba Buhari ya zama gatan marayun Nigeria muna fatan Allah Ya biyashi da Aljannah Madaukakiya Amin
©HausaLoaded
Post a Comment