Shahararren dan wasan Hausa Ali Nuhu ya shaida wa BBC cewa ba sabon abu ne ‘yan fim su shiga harkokin siyasa ba, kamar yadda yanzu ‘yan wasan Hausa suke yi.
Dan wasan ya bayyana mana hakan ne a wata hirar musamman da muka yi da shi a Kano ranar Laraba.

Ya ce an saba ganin ‘yan wasa suna shiga harkokin siyasa a duniya “kuma su zabi bangaren da suke goyon baya.”
“Wannan shi ne dalili na farko da ya sa na ji cewa ni ma wannan karon ya kamata a dama da ni,” in ji shi.

Daga nan ya ba da tabbbacin cewa daukar bangaren da suke yi a siyasa, ba zai jawo cikas ga sana’arsu ba.
“Ni ina ganin idan dai mutum ya dauki bangare kuma yana da hujjarsa ta daukar bangaren ba na jin wannan zai shafe shi. Kuma idan aka yi la’akari da yadda muke siyasar wasu na bangenan nan, wasu kuma suna wan can bangare,” a cewarsa.

Ya ci gaba da cewa: “Saboda haka duk inda ta fadi sha ne. Akwai dai ‘yan uwanmu a kowane bangare.”
Har ila yau, ya ce bambancin siyasar da ke tsakaninsu da abokan sana’arsa bai jawo wata rashin jituwa ba.
A karshe kuma ya ce ba ya tunanin wasu masoyansa za su iya juya masa baya saboda suna goyon bangaren siyasa daban da nasa.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top