Watan Ramadan lokaci ne na kamewa, tsoron Allah, kyautatawa juna, horas da kai ga zama mutanen kirki da kuma fatan cewa zamu jure kasancewa a hakan ko bayan watan ya wuce. Hakika Azumin watan Ramadan ya kan karawa ruhinmu kusanci izuwa ga Allah, sai dai ba a nan alfanunsa ya tsaya ba.

Binciken kimiyya da dama sun nuna cewa azumin watan Ramadan yana taimakawa wajen kara mana lafiyar jiki a bisa wasu dalilai da suka hada da:



1. Samun karin kwanciyar hankali a sakamakon kyawawan halayyar da muke kwatantawa da kara ingancin zamantakewarmu ta hanyar kyauta da kasancewa da ‘yan uwa da abokan arziki a yayin bude baki, da kuma addu’o’in da muke yawaita yi.

2. Samun raguwar sinadarin cholesterol mai saka kiba a cikin jini sakamakon kayan itatuwa da muke yawaita ci da dabino da abinci lafiyayyu da kuma motsa jiki a lokutan tarawih da nafiloli.

3. Samar da hutu ga kayan cikin mu wadanda a kullum a cikin aiki suke dare da rana wajen narkarwa da tace abincin da muke ci. Matsalolin ciki da dama suna haifuwa ne a sakamakon gajiya da kayan cikin ke yi, wannan ya sa samun hutun su na da matukar mahimmanci ga lafiyar mu.

4. Rage yiwuwar kamuwa da cututtuka sakamakon yawan sinadaran vitamins da minerals da muke samu daga kayan itatuwan da muke yawaita ci a watan Ramadan.

Sai Dai Kash…

Da yawa a cikin mu basa morar wadannan alfanu sai dai ma su kara dulmiyar da lafiyar ta su. Bincike ya nuna irin dabi’un da ke haifar da hakan:

1.Cin abinci da yawa lokacin bude baki ko sahur
Cin abinci har kirji ko ba’a lokacin azumi ba yana tattare da illoli da dama wanda suka hada da rashin narkewar abinci har tsahon awanni 8 zuwa 12 a maimakon awanni 1 zuwa 3, kumburin ciki, ciwon madaciya, girman tumbi da sauransu.

Al’adar mu na kokarin cin abincin safe, rana da dare a lokacin daya yayin da muka bude baki ba karamin illa yake haifarwa ga lafiyar mu ba.

2. Gamje gamjen abinci kala daban daban a lokacin bude baki ko sahur
Ba kowanne abinci ke tafiya da wani ba a ciki. Idan akwai tantama, samu Lemon tsami ka zuba a cikin Madara ka ga abinda zai faru. Wani abincin zai iya hana wani narkewa, wani zai iya saka wani tsami, wani zai iya lalata wani a ciki. Shi yasa ake yawan fama da magwas a lokacin azumi. Abinda yake nufi shine, abinci ya fara lalacewa a ciki ya kasa narkewa


Sannan hatsarin ba a nan ya tsaya ba, musammam idan mukayi la’akari da yadda muke kara adadin sinadarin protein da muke ci a lokacin azumi wanda idan yayi yawa ya kan takura koda sosai kuma ya tsote ruwan jikinmu saboda kodar tana bukatar sa wajen aikin ta na tace sinadarin protein din da yayi yawa da kuma fitar da shi ta fitsari. Wannan ya kan haifar wa da koda matsala sosai

Toh duba da wannan, mecece hanyar cin abinci da tafi alkhairi yayin bude baki?

1. Kar a hada kayan itatuwa da abinci a lokaci daya, sam ba sa tafiya tare, saboda kayan itatuwa ba sa daukar lokaci suke narkewa, cin su da abinci yana hana su narkewa har suyi tsami wanda a karshe zai hana su samar da amfanin da suke bayarwa. Za’a iya fara cin su a farko, bayan anyi sallah da adduo’i sai aci sauran abinci.

2. Muyi kokarin kar mu cika ciki har kirji, za’aiya raba abincin zuwa gida biyu ko uku a kuma ci su a lokaci daban daban saboda kar a takura ciki.

3. Kar aci kayan da ke dauke da sinadarin protein da yawa kamar su kwai, nama, da sauransu.

4. A sha ruwa da yawa sosai domin mayar da ruwan jikin da aka rasa.

5. Abinci ya kasance yana da isasshen kayan lambu.
6. Kar aci abinci dab da lokacin kwanciyar barci saboda yana haifar da matsala hana abinci narkewa da kunburin ciki da magwas


Amma fa akula, cin abinci dai dai yadda jiki ke bukata ba yana nufin a ci abincin da baya kunshe da sinadaran gina jikin gaba dayan su ba. Sam sam ba haka nake nufi ba. 

Allah ya sa mu dace, ya karbi ibadun mu. Allah ya sa muci moriyar dukkanin alfanun wannan wata mai albarka.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top