Ciwon hakori ciwo ne mai zuwa da dan karen radadin zafi wanda har ya kan janyo ciwon kai. Ga wasu hanyoyi mafi sauke wajen magance radadin ciwon hakori.


Kayayyakin Da Ake Bukata
– Ruwa
– Gishiri
– Ganye Gwaiba (Guava)
– Kofi
Yadda Ake Hadawa

A farko da za a tafasa ruwan sannan sai a zuba ruwan cikin kofi, daga nan sai a zuwa gishiri cokali 1 na cokalin shayi (wato teaspoon) sai a juya gishirin har sai a bace a cikin ruwan, sannan sai a dauke ganyen gwaiba kwara 2 a saka cikin kofin.


Yadda Ake Amfani Da Maganin
Bayan an hada maganin sai a dauka kofin a kuskure baki da shi har sai ruwa ya taba hakorin da ke ciwo, a yi hakan akalla sau 3 a rana, da yardan Allah za a samu sauki lamari.

Abun kulawa a nan shine za’a yi amfani kofi 1 wajen kuskure bakin a kowane lokaci har sau 3 a rana wato da safe, rana da dare.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top