Tauraron mawakin Hausa kuma sarkin wakar Sarkon Kano, Nazir Ahmad yayi kira ga masu bayar da sadaka da suke daukar hotunan wadanda suka baiwa sadakar su saka a shafukan sada zumunta da cewa su daina.

Nazir dai be bayyana ko da wa yake ba amma ya wallafa wasu hotunan bidiyo a shafinshi na Instagram inda yace, ba cewa yayi kada a yi sadaka ba, abinda yake fada shine idan an yi a daina daukar hoto ana sakawa a shafukan sada zumunta, yace idan ma mutum ya dauki hoton to a jiye a wayarshi ya daina sakawa a shafukan sada zumuntar sai ya rika kallo yana jin dadi.

Yaci gaba da cewa riya zata iya shigowa ciki, idan kuma riya bata shigo ba to zalinci zai iya shigowa ciki tunda zaka dauki hoton mutum ka je kana tallar gidauniyar ka, neman kudi.

Yace saka hoton mutum cin fuskane, yace misali ace sai kaga hoton mahaifiyarka tazo an bata sadaka a shafin yanar gizo, ya zaka ji? Akwai mutane dake son zuwa su karba amma saboda gudun tonon asirin da za'a musu sun kwammace su kwana da yunwa.

Ya kara da cewa idan kana takamar kana raba buhu goma ko sama da haka to akwai me raba buhu dubu amma baya irin wannan abu, kuma ba kaza ba zuma ko kilishi kake rabawaba amma kake wannan abu.

Kalli bidiyon anan kasa dan jin cikakken jawabin na Nazir:

Danna nan dan kallon bidiyon

Post a Comment

 
Top