Fitaccen mawaki Nazir M. Ahmad ya caccaki mutanen da idan za su ba da sadaka sai su rika daukar hotunan mutanen da suka ba sadakar sannan su rika yadawa a kafafen sada zumunta.
Mawakin wanda shi ne Sarkin Wakar San Kano, ya yi caccakar ce a wani bidiyo mai tsawon minti uku da ya turo wa Aminiya a ranar Talatar da ta gabata.

Mawakin ya ce ba wai cewa ya yi kada mutum ya yi sadaka ba, abin da yake nufi shi ne idan za a bayar da sadakar to kada a dauki hoton wadanda ake ba sadakar har a kai ga yadawa a kafafen sadarwa.
Ya ce, “Kada ka dauki hoto, don Allah kada ka bari a dauki hoto, in kuma ka dauka, ko ka bari aka dauka, to ka bar shi a wayarka ka rika gani ka ji dadi, in ka tara abin da za ka bayar duka ka dauka a hoto ka ce wa mutane zan raba wannan abin, haka ya fi sauki.


“Amma wanda za ka ba ka dauke shi ka dora a kafar sadarwa, wannan ne na ce kada ka yi, saboda bai kamata ba kwata-kwata, ka sa a ranka a ce wannan babarka ce aka ba sadaka aka dauke ta a hoto, sannan a ce ka shiga Social Media kawai sai ka ga hoton babarka ta mika hannu biyu za a ba ta shinkafa yaya za ka ji a ranka? To Allah ba zai ji dadi ba, mu ma ba za mu taba jin dadin wannan tonon asirin ba,” inji shi.

Sarkin Waka ya bayyana dalilin da ya sa sa ya ce haka shi ne, akwai mutanen da suke raba buhu dubu amma ba sa yadawa a kafar sadarwa saboda ba sa so riya ta shigo ciki.
Ya ce, “In ma buhu 100 kake rabawa, to akwai masu raba buhu dubu, amma sun taba daukar hoto sun nuna? Ba sa yi, babu, kada riya ta shigo cikin aikinmu, idan ma riya ba ta shigo ba, to tonon asiri ya shigo, idan tonon asiri bai shigo ba, to zalunci ya shigo.”

“Ka ba mutum shinkafa ta wata daya, ka dauki hotonsa ka je kana tallar gidauniyarka na (tsawon) shekara biyu, neman kudi, to ka ga zalunci ya shiga. To jama’a mu kiyaye, mu daina cin mutuncin ’yan uwanmu talakawa, wadansu suna so su zo su karba, amma wallahi gudun kada a yi musu tonon silili gara su kwana da yunwa,” inji shi.

Ya ce, “Kai ba kaji kake rabawa ba, ba zuma ba, ba kilishi ba, in ma kudi ne nawa suke? In a ce Naira miliyan uku-uku kake rabawa, ka sa kyamara sai mu tura mutane su je su karba, har mu ma sai ka gani a layi, saboda abu kake rabawa mai dan nauyi, to Naira miliyan uku ma nawa take idan ka ba dan Adam ita, ka sani cinyewa zai yi. Ya kamata a rufa wa mutane asiri.”

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top